Shugaban kasa a 2023: Saraki ya cancanci darewa kujerar Buhari, in ji kungiyar matasa
- Dubban matasa a jihar Kwara sun yi gangami a manyan unguwannin Ilorin, jihar Kwara domin nuna goyon bayansu ga takarar shugabancin Bukola Saraki a 2023
- Matasan sun bayyana cewa Saraki ne ya fi cancanta ya zama shugaban kasa duba ga cewar yankin arewa ta tsakiya bai taba shugabanci ba a kasar
- Sun kuma ce tsohon shugaban majalisar dattawan zai hada kan kasar tare da bunkasa tattalin arzikinta
Kwara - Dubban matasa a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, sun yi gangami a manyan unguwannin Ilorin, jihar Kwara domin nuna goyon bayansu ga takarar shugabancin Bukola Saraki, jaridar Punch ta rahoto.
Matasan karkashin inuwar kungiyar Grow Nigeria Youth Movement, sun hadu a filin wasa na jihar Kwara tun da misalin karfe 7:00 na safe inda suka zagaya yankunan Taiwo, Unity, Challenge da Post Office kafin su tsaya a gidan tsohon shugaban majalisar dattawan da ke GRA.
Yanzu: Buhari, Jonathan da sauran manyan 'yan Najeriya sun hallarci wurin bikin zagayowar ranar haihuwar Anyim
Da yake jawabi ga taron a madadin Saraki, shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon kakakin majalisar jihar, Babatunde Mohammed, ya ce abun da matasan suka yi ya yi daidai da kiraye-kirayen da ake yi kan yankin arewa maso tsakiya ya samar da shugaban kasa kuma a hadu a kan Saraki.
Mohammed ya bukaci sauran yan takaran shugaban kasa a jam’iyyar da su marawa Saraki baya, wanda a cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Shine ya fi cancanta da sanin makamar hada kan kasar, musamman a wannan lokaci da mu ke fama da rarrabuwar kawuna.
“An gwada Saraki kuma an gani a kasa, sannan ya nuna kwarewa tare da abubuwan da ake bukata a majalisar zartarwa da na dokoki wanda za su iya mayar da Najeriya kan tafarkin ci gaban tattalin arziki da hadin kan addini da kabilanci."
Mohammed ya ce arewa ta tsakiya shine yanki guda da bai taba shugabancin kasar ba sannan yay i kira ga sauran yankuna da su mara masa da Saraki baya don adalci da daidaito.
A nasa bangaren, jagoran kungiyar Grow Nigeria Youth Network kuma wanda ya shirya gangamin, AbdulHamid Mohammed, ya ce sun yi taro da matasa a fadin kasar daga kokarinta na tuntuba, rahoton Daily Trust.
Ya ce Saraki na da iyali, addini da tushen da suka dace domin hada kan kasar.
IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito
A gefe guda, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa ga burin Saraki na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Janar Babangida ya yi martani ne kan bukatar da wakilan Abubakar Bukola Saraki da suka samu jagorancin shugaban kungiyar kamfen din sa, Farfesa Hagher Iorwuese da darakta janar, Osaro Onaiwu wadanda suka je har gidan IBB da ke Minna domin neman goyon baya.
Babangida wanda ya kasa boye kaunarsa ga Saraki, ya kasa rufe baki don kai tsaye ya ce Saraki tamkar bindigar yaki ce mai harba kanta, a takaice hakan ne kwatancen Saraki, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng