Da Dumi-Dumi: Buhari ya ɗage ganawarsa da gwamnonin APC bayan sun hallara
- Shugaba Buhari ya soke ganawar da aka shirya zai yi da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a fadarsa Aso Villa, Abuja
- Tuni dai wasu gwamnonin suka samu hallara domin gudanar da taron, yayin da shugaban ke shirin kama hanya zuwa Turai
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya samu gana wa da Buhari kan matsalolin da suka shafi jiharsa
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ɗage zamansa da gwamnonin APC wanda aka shirya gudanarwa yau a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Vanguard ta rahoto cewa duk da ba'a bayyana abin da za'a tattauna a wurin taron ba, wata Majiya tace taron ba zai rasa nasaba da babban gangamin APC da zai gudana ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin gwamnonin sun fara hallara a fadar shugaban ƙasa, sannan suka gano taron ba zai gundana ba.
Babu wani cikakken bayani kan dalilin ɗage taron, amma an shirya tsarin ayyukan shugaban ƙasan ya ƙare da wuri, domin zai tafi ƙasar Belgium halartar taron kawancen AU da EU, Dail Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga cikim gwamnonin da aka hangi sun ɗira fadar shugaban ƙasan akwai Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Simon Lalong na jihar Filato, Ben Ayade na Cross Riba, Malam El-Rufa'i na Kaduna, Hope Uzodinma na Imo da Yahaya Bello na Kogi.
Sauran waɗan da aka hanga sun hallara sun haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omon Agege, da mataimakin kakakin majalisar dokoki, Ahmed Wase.
Ko ya gwamnonin suka ji?
Ɗaya daga cikin gwamnonin, gwamnan Imo, Hope Uzodinma, wanda ya samu ganawa da Buhari kan lamurran da suka shafi jiharsa, ya ce ba wani abun damuwa bane idan APC ta sake ɗaga ranar babban taron ta.
Da yake amsa tambayar manema labaran gidan gwamnati game da tsarin raba kujerun shugabannin APC da suka gaza cimma matsaya, gwamnan ya ce:
"Gaskiya a matsayar da jam'iyya ta ɗauka, ba wani abu bane dan an sake ɗage ranar babban taron, abun da ya fi amfani a wurin mu shi ne wajibi muyi taron wata rana."
"Mun saka ranar 26, idan wani abu ya taso zamu iya matsar da shi. Abin da muka sa a gaba muka maida hankali a kai shi ne gina demokaradiyya a Najeriya."
A wani labarin kuma Ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, ya bukaci matasan Najeriya sun maida hankali kan samun kwarewa fiye da takarda
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, ya shawarci matasa sun bai wa samun kwarewa fifiko.
Pantami yace idan matasa suka samu horo kuma suka zama gwanaye, duk wasu kalubalen kasar nan za su zama tarihi.
Asali: Legit.ng