Zamfara: Kotu ta yi watsi da bukatar mataimakin gwamna Matawalle da jam'iyyar PDP
- Babbar kotun tarayya a Abuja ta ƙi amincewa da bukatar mataimakin gwamnan Zamfara da PDP na sabunta hukuncin bara
- A bara dai, Kotun ce ta yi umarnin dakatar da majalisar dokokin jihar cigaba da shirin tsige Mahdi Gusau, mataimakin gwamna
- Tun bayan sauya sheƙar gwamna Matawalle zuwa APC, saɓani ke shiga tsakanin sa da mataimakinsa
Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta yi fatali da bukatar mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi Aliyu Gusau, da jam'iyyarsa ta PDP.
Premium Times ta tattaro cewa Mahdi Gusau ya bukaci kotun ta dakatar da shirin tsige shi da majalisar dokokin jihar ta fara yi kwanakin baya.
Alƙalin kotun, Mai Shari'a Inyang Ekwo, ya yi watsi da bukatar lauyoyin mataimakin gwamnan, da jam'iyyarsa ranar Litinin.
Maimakon haka alƙalin ya saka ranar 10 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar da za'a dawo don cigaba da fafata shari'ar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A shekarar da ta gabata, gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya fice daga jam'iyyar PDP, wacce ta taimaka masa ya hau mulki, zuwa APC.
Mista Mahdi Gusau, ya ƙi bin sawun uban gidan nasa zuwa APC, wanda ake ganin haka ne ya haifar da saɓani tsakanin mutanen biyu.
Domin nuna biyayya ga gwamna, Majalisar dokokin jihar ta yi yunkurin tsige mataimakin gwamnan daga kujerarsa a shekarar da ta gabata bisa laifin saɓawa doka.
Babban zargin da yan majalisun suka rataya wa Mahdi shi ne ya gudanar da zagayen siyasa duk da rashin tsaron da ake fama da shi, amma ya musanta.
Kotu ta hana majalisa a bara
Sai dai babbar Kotun tarayya dake Abuja, a watan Yuli, 2021, ta dakatar da yan majalisun da babban Alƙalin jihar daka kokarin tsige mataimakin gwamnan.
Amma a halin yanzun majalisar dokokin ta sake sabon shirin tsige Mahdi Gusau daga kujera a farkon watan nan.
Makonni kalilan da suka shuɗe majalisar ta aike wa mataimakin gwamnan da sakon shirin da take na tsige shi.
Wane mataki Mahadi ya ɗauka?
Bisa wannan lamarin ne, Mataimakin gwamna da kuma PDP suka sake garzaya wa Kotu, suka bukaci ta sabunta umarninta na 2021 na dakatar da yunkurin majalisa.
Bayan doguwar mahawara tsakanin ɓangarorin biyu, Alkalin kotun ya ɗage zaman har zuwa wata mai kamawa, kamar yadda The Cable ta rahoto.
A wani labarin kuma Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC
Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe na ƙara kamari, inda lamarin ya fara shafar gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya.
Hadimin gwamna mai bada shawara kan harkokin gwamnati, Jijji Gadam ya yi murabus daga muƙaminsa nan take.
Asali: Legit.ng