Gwamnoni suna fake wa da Buhari domin ɓoye rashin ƙwazon su, Femi Adesina

Gwamnoni suna fake wa da Buhari domin ɓoye rashin ƙwazon su, Femi Adesina

  • Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari na masamman, Femi Adesina ya zargi wasu gwamnoni da fakewa da Buhari wurin boye rashin kwazon su
  • A cikin wani rubutu da ya saki a shafinsa na Facebook wacce ya yi wa take ‘Zulum Zooms In’ a ranar Alhamis ya ce wasu gwamnonin ba sa yin abubuwan da suka dace sai su bige da daura laifin kan Buhari
  • Ya kara da bayyana yadda Buhari yake da sakewa da kowa har da masu caccakar sa cikin gwamnonin amma duk da haka suka zabi mayar masa da laifukan su

Mai ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari na musamman, Femi Adesina ya zargi wasu gwamnoni da fake wa da Buhari wurin boye rashin kwazon su, The Punch ta ruwaito.

A wata wallafa wacce Adesina ya saki a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, mai taken, ‘Zulum Zooms In’ ya kula da yadda gwamnonin suke mayar da laifi akan Buhari ko da suna da hannu a ciki.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun caccaki hadimin Buhari saboda rubutun da ya wallafa a Twitter

Gwamnoni suna amfani da Buhari wurin ɓoye rashin ƙwazon su, Femi Adesina
Femi Adesina da Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ya ce shugaban kasa a sake yake da kowa har da masu caccakarsa cikin gwamnonin amma duk da hakan sun zabi mayar da suka akan sa.

A cewarsa, akwai gwamnonin da suke zagin sa kuma su nufi fadarsa don neman mafaka amma duk da haka kofar sa a bude take gare su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zargi wasu gwamnoni da kalmashe albashin mutanen su su daura laifin akan Buhari

A cikin wallafar, Adesina ya kara da cewa:

“Wasu gwamnoni su na tunanin wata nasara ko jarumta suke yi idan sun soki shugaban kasa. Idan sun rike albashi da fanshon jama’a sai su daura laifin akan Buhari duk don su kawar wa mutanensu hankali daga fansho da albashin.
“Babu titin da suka gina, duk Buhari ne yake yi. Duk wasu kayan more rayuwa sun rube a gaban idanun su. Sun kasa kare jama’an su kuma sun daura laifin akan Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, Sanatoci, tsofaffin masu mulki 100 sun hadu domin ceto Najeriya kafin zaben baɗi

“Idan sun yi hakan gani suke yi zai janyo musu hankalin jama’a. Amma ina, wahala kawai mutanen su suke sha saboda yunwa kuma sun san ta inda matsalar take.”

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164