Zaben 2023: Wani babban jigon arewa ya goyi bayan Tambuwal ya tsaya takarar shugaban kasa
- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto na kara samun karbuwa a kudirinsa na son zama shugaban kasa a 2023
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya yi kira ga jam'iyyar PDP da ta mallakawa Tambuwal tikitin takarar shugaban kasarta
- Bafarawa ya ce gwamnan Sokoton shine mutum mafi cancanta da wannan kujera saboda gogewarsa a harkokin shugabanci
Kebbi - Gabannin babban zaben 2023, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya marawa takarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal baya.
Bafarawa ya bayyana cewa gwamnan na jihar Sokoto ya cancanci mallakar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
A cewar Bafarawa, Tambuwal na da damar darewa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda yana da gogewa a dukka bangarorin gwamnati guda uku.
2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron neman shawarwari na Tambuwal a Kebbi, a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Daily Post ta nakalto Bafarawa yana cewa:
"Ba wai dan majalisa bane kawai a'a Tambuwal ya kasance lauya ne, inda hakan ke nufin ya dace da bangaren shari'a sannan a lokaci guda ya kasance gwamna mai ci a yau wanda ke a wa'adinsa na biyu.
"Hakan na nufin fada maku cewa Tambuwal ya dace da dukka bangarori uku na gwamnati. Don haka, shi yafi cancanta ya mallaki tikitin shugabancin kasar.
"Shiyasa muka kasance a nan don kai shi inda muke so ya kasance, ba wai inda yake son kasancewa ba."
Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal
A gefe guda, mun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tabbacin cewa kwanan nan za ta tarbi masu sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa gabannin zaben 2023.
Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, yayin ziyararsa ta uku kan neman shawara game da kudirinsa na neman tikitin shugaban kasa na PDP a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, jaridar The Nation ta rahoto.
Gwamnan ya ziyarci Bamaina a jihar Jigawa da Gusau a jihar Zamfara tun a makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng