Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya magantu kan makomar siyasar kasar gabannin zaben 2023
  • A yayin ziyarar da ya kai jihar Kebbi a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, Tambuwal ya yi hasashen cewa APC za ta fuskanci gagarumin sauya sheka kwanan nan
  • Gwamnan ya kuma ce PDP za ta lallasa abokan adawarta a zaben 2023 mai zuwa

Kebbi - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tabbacin cewa kwanan nan za ta tarbi masu sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa gabannin zaben 2023.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, yayin ziyararsa ta uku kan neman shawara game da kudirinsa na neman tikitin shugaban kasa na PDP a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Najeriya yanzu na rugujewa hannun jahilan Shugabanni, marasa hangen nesa, IBB

Gwamnan ya ziyarci Bamaina a jihar Jigawa da Gusau a jihar Zamfara tun a makon da ya gabata.

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal
Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal Hoto: Punch
Asali: UGC

Tambuwal wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa; tsohon mataimakin gwamnan Sokoto, Mukhtar Shagari da tsohon ministan lantarki, Injiniya Bello Suleiman, ya yaba da hadin kan da jiga-jigan PDP a Kebbi da mabiyansu suka nuna a zaben karamar hukuma da aka yi kwanan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“PDP a jihar Kebbi na da hadin kai. PDP a jihar Kebbi na da karfi. Ina rokon Ku da Ku yi aiki tare a matsayin iyali guda domin janyo hankalin karin mutane daga masu adawa saboda akwai matsala a daya gidan.
“Na san za su sauya sheka sannan su dawo nan. Idan suka zo ina shawartanku da ku zamo a hade ta yadda idan suka zo, za Ku kasance masu mutuntawa da tafiya tare da kowa, ta yadda Za mu lashe zabe da izinin Allah a nan jihar Kebbi da Najeriya a 2023."

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan Arewa dake son gaje kujerar Buhari ya shiga Kebbi, ya samu gagarumin goyon bayan PDP

Tambuwal ya koka kan yadda Najeriya ke shirin rugujewa sakamakon rashin tsaro, tsarin kiwon lafiya mara inganci, talauci, tabarbarewar ilimi, cin hanci da rashawa da sauran yanayi da gwamnatin APC ta jefa kasar a ciki.

Bafarawa wanda ya bayyana ziyarar a matsayin na gida, ya nuna farin ciki da karamcin da PDP reshen jihar Kebbi ta nuna a yayin zaben kananan hukumomi a jihar.

Da yake tuna rawar ganin da Tambuwal ya yi a matsayin kakakin majalisar wakilai da kuma gwamnan jihar Sokoto, Bafarawa ya ce:

“Wannan ne dalilin da yasa nake mara maka baya domin ka samu tikitin shugaban kasa na PDP a 2023.
“Za a iya hasashen nasarar hakan a kan zabin wakilai na jam’iyyar. Muna da tabbacin wakilan PDP a Kebbi za su zabe shi, kamar yadda ya tuna cewa a 2019 su uku - shi, Kabiru Tabimu Turaki da Tambuwal duk sun nemi matsayi daga na neman tikitin shugaban kasa a PDP kuma Tambuwal ne ya zo na biyu.”

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

A yanzu, ya bayyana cewa daga shi har Turaki wadanda suka marawa Atiku Abubakar baya wajen samun tikitin a wancan lokacin, sun shirya yin aiki tare da Tambuwal.

Zaben 2023: Duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa ba zata samu nasara ba, Gwamnan APC

A wani labarin, Shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (SAN), ya yi gargaɗin cewa duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa a takarar shugaban ƙasa ba zata yi nasara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a ofishinsa, yayin da ya karɓi baƙuncin kungiyar Power Rotation Movement, bisa jagorancin shugaba, Dakta Pogu Bitrus.

Akeredolu yace duk ma su nuna adawa da tsarin mulkin karɓa-karba to ba su ƙaunar Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya kuma tsintsiya ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng