2023: Gwamnonin arewa biyu sun garzaya fadar shugaban ƙasa, sun saka labule da Buhari
- Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tare da gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, sun gana da Buhari
- Gwamnonin sun ziyarci fadar shugaban ƙasa ne domin tattauna wa game da babban taron APC na ƙasa dake tafe a watan Fabrairu
- Tuni uwar jam'iyyar karkashin kwamitin Mala Buni na jihar Yobe ta fara shirye-shiryen taron ranar 26 ga wata
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata, ya karɓi baƙuncin gwamnonin jam'iyyar APC guda biyu a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnonin sune, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, shugaban kungiyar gwamnonin APC a karo na biyu, da kuma Muhammad Badaru na jihar Jigawa.
Gwamnonin sun gana da shugaban ƙasa Buhari ne dangane da babban gangamin APC na ƙasa dake tafe ranar 26 ga watan Fabrairu, wanda za'a zaɓi shugabannin jam'iyya a matakin ƙasa.
A ranar Alhamis da ta gabata, jam'iyyar APC ta rantsar da sabbin shugabanninta na jihohi yayin da take fuskantar babban taro.
Mambobi dake takarar zama shugaban APC na ƙasa na cigaba da yaƙin neman zaɓe da goyon baya a faɗin Najeriya.
Ƙungiyoyi da dama na cigaba da taro kala daban-daban a wani yunƙurin da suke na ganin wanda suke goyon baya ya samu nasara.
Sai dai a ɓangaren shugaban ƙasa Buhari ya yi gum da bakinsa game da wanda yake so ya zama shugaban jam'iyya na ƙasa da kuma wanda zai gaje shi a 2023 dake tafe.
Wane shiri APC take yi game da taron?
A yanzun, Uwar jam'iyya ta ƙasa ta kaddamar da kungiyar Kansiloli da aka zaɓa karkashin inuwar APC domin su fara tattaro kan mambobi da masoyan jam'iyyar tun daga tushe.
Shugaban kwamitin riƙon kwarya, Gwamna Mala Buni, shine ya kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin Kansilan gundumar Guringawa, karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano, Muslihu Yusuf Ali.
Buni, wanda ya samu wakilcin Daraktan shirye-shirye na APC, Alhaji Alpha Yahaya, ya ce:
"Mun san cewa siyasa na can ƙasa, kuma mun fahimci cewa siyasar gaske ita ce wacce aka ɗakko tun daga tushe, wannan dalilin yasa ba zami wasa da Kansiloli ba."
"Abin da muke so ku saka a gaba shi ne ku haɓaka jam'iyyar mu ta APC tun daga tushe ta yadda mutane zasu amince da ita a yankunan mu."
A wani labarin kuma Gwamnan Arewa dake son gaje kujerar Buhari ya shiga Kebbi, ya samu gagarumin goyon bayan jam'iyyar PDP
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kai ziyara jihar Kebbi game da kudirinsa na neman shugaban ƙasa a 2023.
Gwamnan ya gana da shugabannin PDP na jihar, kuma sun amince sun tabbatar masa da goyon bayan ya dare kujera lamba ɗaya.
Asali: Legit.ng