2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB
- Tawagar jam'iyyar PDP sun gana da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida
- Dr. Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar na kasa ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan tsohon shugaban kasar da ke unguwar Hilltop a garin Minna, jihar Neja
- Ana ganin ziyarar tasu ba za ta rasa nasaba da babban zaben 2023 da ke tunkarowa ba
Minna - Manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun kaiwa tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin sojoji, Ibrahim Badamasi Babangida, ziyarar bangirma.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan tsohon shugaban kasar da ke unguwar Hilltop a garin Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu.
A cikin hotunan wanda jaridar Leadership ta wallafa, an gano tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye a cikin tawagar.
Sauran wadanda ke a tafiyar sun hada da mataimakin shugaban PDP na kasa a arewa, Cif Tom Ikimi, tsohon gwamna Nwodo, sakataren labaran jam’iyyar na kasa da kuma shugabar matan jam’iyyar na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan dalilin ziyarar tasu, sai dai ana ganin ba zai rasa nasaba da babban zaben 2023 da ke gabatowa ba.
IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito
A wani labarin, mun ji cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa ga burin Bukola Saraki na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Janar Babangida ya yi martani ne kan bukatar da wakilan Abubakar Bukola Saraki da suka samu jagorancin shugaban kungiyar kamfen din sa, Farfesa Hagher Iorwuese da darakta janar, Osaro Onaiwu wadanda suka je har gidan IBB da ke Minna domin neman goyon baya.
Babangida wanda ya kasa boye kaunarsa ga Saraki, ya kasa rufe baki don kai tsaye ya ce Saraki tamkar bindigar yaki ce mai harba kanta, a takaice hakan ne kwatancen Saraki, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng