Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya magantu a kan halin da kasar ke ciki a yanzu
- Wike ya ce akwai bukatar jam'iyyar PDP ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC domin daidaita abubuwa
- Ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi bayan ya dawo daga kasar waje inda ya je jinya
Kaduna - Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya bayyana Najeriya a matsayin kasa da ke zubar jini.
Wike wanda ya kasance a Kaduna a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da su hada kansu domin kwace mulki a 2023, Vanguard ta ruwaito.
Mai masaukin baki kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya fada ma Wike da mukarrabansa cewa mutanen Najeriya ba za su ji dadi ba idan PDP ta ki hada kanta ta kwace mulki.
Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara
Ya ce duba ga sakamkon zabe na baya-bayan nan inda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sha kaye a mazabu da dama a matakan farko, yan Najeriya sun gaji kuma suna jiran PDP ta karbi ragamar shugabanci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wike ya fada ma dandazon jama’ar cewa ya je gidan Makarfi na Kaduna ne don ganinsa, cewa ba tafiyar siyasa bace illa don ganin sanatan wanda ya je kasar waje bisa dalili na rashin lafiya.
A cewarsa, Makarfi na da muhimmanci kuma yana da gurbi mai girma a wajen yan PDP saboda irin shugabanci nagari da ya nuna don ceto jam’iyyar lokacin da aka yi amfani da Ali Modu Sheriff don tarwatsa jam’iyyar, rahoton Nigerian Tribune.
Ya yi bayanin cewa yakamata mambobin jam’iyyar su nuna kulawa game da hadin kai da dorewar jam’iyyar, sannan su hade gabannin kamfen mai zuwa domin kwace mulki daga hannun APC mai mulki.
Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari
A gefe guda, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa baya tunanin akwai wani mutum da ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya sama da shi.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, a yayin wata hira a shirin Channels TV na Politic Today.
Yace duba ga shaidar da ya samu a matsayin minista da kuma gwamnan jiha mai arzikin mai, yana da gogewar da ake bukata don shugabantar kasar.
Asali: Legit.ng