Shahararren Malamin Musulunci a Kano da wasu Manyan Farfesoshi 8 sun shiga jam'iyyar siyasa
- Babban malamin addinin musuluncin nan a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, bayan ficewa daga APC, ya koma jam'iyyar ADC
- Shugaban ADC reshen Kano, wanda ya tabbatar da haka, yace Malamin ya shiga tare da wasu manyan Farfesoshi 8
- Yace nan ba da jimawa ba, Hedkwatar ADC ta ƙasa zata shirya babban taro domin karɓan sabbin mambobin
Kano - Fitaccen malami kuma shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Shiekh Ibrahim Khalil, ya shiga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).
Shugaban ADC reshen jihar Kano, Musa Shuaibu Ungogo, shi ne ya tabbatar haka ga manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa Malamin tare da wasu manyan Farfesoshin Ilimi da ba'a faɗi bayanan su ba guda 8, sun zama cikakkun mambobin jam'iyyar ADC.
Meyasa suka shiga ADC?
Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa manyan mutanen sun ɗauki matakin shiga ADC ne domin ceto Kano daga mulkin kama karya, ta'amali da miyagun kwayoyi da bara a kan titi da sauran kalubale.
Ungogo ya sanar da cewa ba da jimawa ba, uwar jam'iyyar ADC ta ƙasa zata shirya gagarumin taro domin karrama shigowarsu cikin jam'iyya.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Sheikh Khadil, tsohon hadimin gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, kuma mamban APC ya fice daga jam'iyyar ne watan da ya gabata.
Meyasa ya bar APC mai mulki?
Malamin ya bayyana cewaya ɗauki matakin fita daga APC mai mulki ne saboda rikicin da yaƙi ci yaƙi cinye wa a cikinta.
Rikici ya barke tsakanin shararren malamin da kuma gwamnatin jihar Kano, tun bayan da ya bar muƙaminsa na mai baiwa gwamna shawara ta musamman.
Lamarin da ya kusa yin awon gaba da kujerar Khalil ta shugaban majalisar malamai a Kano, amma daga bayan gwamnatin Kano ta musanta zargin.
A wani labarin na daban kuma Ɓarayi sun fasa Hostel ɗin mata a jami'ar BUK, sun aikata mummunar ta'asa
Wasu Barayi sun kutsa cikin dakin kwanan ɗalibai mata a jami'ar Bayero University Kano, sun sace manyan wayoyi.
Ɗaliban da lamarin ya shafa sun shiga matuƙar damuwa, domin har da sabbin wayoyin IPone daga cikin waɗan da aka sace.
Asali: Legit.ng