Sauya sheƙa: Jerin Sanatocin Jam'iyyar PDP 6 da suka koma APC

Sauya sheƙa: Jerin Sanatocin Jam'iyyar PDP 6 da suka koma APC

A ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, mataimakin marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Emmanuel Bwacha, ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma All Progressives Congress (APC).

Bwacha, mai wakiltar Jihar Taraba ya sanar da komawarsa APC ne a lokacin da ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Sauya sheƙa: Jerin Sanatocin Jam'iyyar PDP 6 da suka koma APC
Jerin Sanatocin Jam'iyyar PDP 6 da suka koma APC. Hoto: @Abuja_Facts, @seunokin, @Guarantor2011, @SenatorYau, @AnkaDealer, @Ifeyinwanwobi2
Asali: Twitter

Sanatan na Taraba Central ba shine na farkon komawa APC ba a baya-bayan nan. Tun bayan babban zaben shekarar 2019, a kalla Sanatocin PDP biyar ne suka koma jam'iyyar APC.

Ga jerin sunayensu:

1. Sanata Stella Oduah (Anambra North)

A ranar Alhamis, 26 ga watan Agustan 2021, Sanata Stella Oduah, Yar Majalisar mai wakiltan Anambra North ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin mutum 7 da Buhari ya nada a hukumar INEC, majalisa ta tabbatar

Oduah, tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama ta koma ne jim kadan kafin zaben gwamnan Anambra ta Nuwamban 2021.

Amma, komawarta bai taimakawa APC yin nasara a zaben ba.

2. Elisha Abbo (Adamawa North)

Sanata Elisha Ishaku Abbo ya sanar da komawarsa APC cikin wasikar da ya aike wa Majalisar a ranar Laraba 5 ga watan Nuwamban 2020, kimanin shekara daya bayan zabensa a karkashin jam'iyyar PDP.

Bayan komawarsa, Abbo, wanda ke wakiltar Adamawa North ya bayyana niyarsa na yin takarar gwamna a 2023.

3. Peter Nwabaoshi (Delta North)

A ranar Juma'a, 25 ga watan Yunin 2021, Sanata Peter Nwaboshi ya bar PDP ya koma APC.

Buhari Sallau, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar da komawarsa APCn.

Hakan ya faru ne bayan Sanatan na Delta North ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari tare da shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aikawa Majalisa sunayen sababbin mukaman da ya nada a Gwamnati

4. Sahabi Ya'u (Zamfara North)

A ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, aka sanar da komawar Sanata Sahabi Yau zuwa Jam'iyyar APC.

Ya bayyana cewa ya koma APC ne saboda rikicin cikin gida, mulkin kama karya da rashin shugabanci na gari a PDP.

5. Lawali Anka (Zamfara West)

Sanata Lawali Anka wanda ya koma APC daga PDP a Yunin 2021. Kamar Ya'u, Sanatan na Zamfara West shima ya bayyana cewa rikicin cikin gida, mulkin kama karya da rashin shugabanci na gari a PDP ne yasa ya koma APC.

6. Emmanuel Bwacha (Taraba Central)

Kamar yadda bayyana tunda farko, mutum na baya-bayan nan da ya fice daga PDP ya koma APC shine Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa, Emmanuel Bacha.

Akwai yiwuwar wasu sanatocin su sauya sheka musamman a yanzu da aka tunkarar babban zaben kasa a 2023.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

Kara karanta wannan

Masha Allah: NUC ta amince wa BUK fara yin digiri a fanin Shari'ar Musulunci

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164