Mahdi Gusau: 'Yan majalisa suna shirin tsige mataimakin gwamnan Zamfara kan zargin rashawa
- ‘Yan majalisar Jihar Zamfara sun fara shirye-shiryen tsige mataimakin gwamnan jihar tun bayan mataimakin kakakin ya gabatar wa majalisar takardar korar shi
- Mataimakin kakakin majalisar, Musa Bawa ya gabatar wa da kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu takardar a ranar Juma’a a Gusau, babban birnin jihar
- An samu bayanai dangane da yadda majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da yin karantsaye ga kundin tsarin mulkin jihar da kuma amfani da matsayinsa wurin yin sata
Jihar Zamfara - Yan Majalisar Jihar Zamfara sun fara shirye-shiryen tumbuke mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Gusai, daga mukamin shi, Channels TV ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan wata takarda ta kora ga mataimakin gwamnan wanda aka gabatar ga kakakin majalisar.
Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar, Musa Bawa, ya gabatar da takardu ga kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu a ranar Juma’a a farfajiyar majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai ba a san dalilin mataimakin kakakin majalisar ba wanda ya maimaita shugabancin kwamitin asusun gwamnati ba na daukar wannan matakin.
Ana zargin Mahdi da handamar dukiyar al’umma
Channels TV ta tattaro bayanai akan yadda majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da yin karantsaye ga kundin tsarin mulki, tozarta mukaminsa da kuma satar kudade.
A cewar Bawa yayin gabatar da takardun a wani kwarya-kwaryan taro da suka yi a ofishin kakakin:
“Ina gabatar da wannan takardar ga kakakin majalisa, Nasiru Mua’zu Magarya akan tumbuke mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.”
Lokacin da Mu’azu ya amshi takardun ya yi alkawarin duba takardun inda yace zai dauki mataki daidai da abinda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.
Sun fara samun matsaloli ne tun bayan gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya koma APC
A cewarsa:
“Ka zo nan ofishi na, mataimakin kakakin majalisa kuma shugaban kwamitin asusun gwamnati, kuma ka gabatar min da takardun cire mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau.
“Na amsa kuma ina mai tabbatar muku da cewa zan yi aiki bisa yadda kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka gyara a 1999 ya tanadar.”
Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ci gaba da nuna rashin yardarsa akan abubuwa da dama tun bayan gwamnan ya sauya jam’iyya.
Matawalle ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar PDP kuma tun watan Yunin shekarar da ta gabata ya sanar da komawarsa APC.
Yayin da kowa ya yi tunanin mataimakinsa zai bi sahun sa, Gusau ya bayyana a taron PDP inda ya ce yana nan a jam’iyyar babu gudu babu ja da baya.
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Asali: Legit.ng