Babu wanda ya isa ya kai tikitin takarar shugaban kasa wani yanki, Sule Lamido
- Jigon jam'iyyar hamayya PDP, Sule Lamiɗo,ya yi fatali da batun tsarin mulkin karba-karba yayin fitar da ɗan takara
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Najeriya na bukatar nagartaccen jagora wanda jama'a suke kauna
- A cewar Lamiɗo, abun da takaici ka ga wani cikakken ɗan Najeriya mai kishin ƙasa amma ya ɓushe da kiran a kai tikiti wani yanki
Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, yace babu wanda ya isa ya yanke hukunci kan tikitin shugaban ƙasa a 2023 na PDP saboda dalilansa na kabilanci.
The Nation ta rahoto tsohon ministan harkokin waje na cewa jam'iyya zata zaɓa ta darje wajen tsayar da ɗan takara mai nagarta da kuma jama'a.
Lamiɗo ya yi wannan furucin ne a mahaifarsa Bamaina a jihar Jigawa, lokacin da Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya ziyarce shi domin shawari da goyon baya.
Tsohon gwamnan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abun na damu na kuma ya sani takaici ganin yadda cikakken ɗan Najeriya mai ƙaunar haɗin kai da cigaban ƙasa, ya koma gefe yana sanya kabilanci, addini da banbancin yanki wajen fitar da jagoran Najeriya."
"Babu wanda zai kai wani mukami zuwa wani yankin kasa saboda son rai ko yana son yi wa mutane barazana. Ba mu yarda ba kuma ya saɓa wa demokaradiyya, sannan ba zamu taɓa bari haka ta faru ba.
Wane cikakken ɗan Najeriya ne ya nemi haka?
A ranar Talata, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ƙara jaddada cewa kudu ya dace jam'iyyar PDP ta kai tikitin ta na shugaban ƙasa, saboda a samu ɗan yankin ya gaji Buhari.
Wannan furuci na gwamna Wike ya sa ake ganin kalaman Sule Lamiɗo martani ne kai tsaye zuwa ga ikirarin gwamnan.
Da yake fira da Channels tv da daddare Lamiɗo yace:
"A baya mun rungumi mulkin karɓa-karba saboda samar da daidaito a siyasance, amma yanzun muna bukatar watsi da wannan tsarin, kamata ya yi mu zaƙulo jagora, wanda aka jaraba aka gani a ƙasa."
"Tsarin karba-karba ba sabon abu bane a Najeriya. Amma ya kamata mu duba demokaraɗiyya, Najeriya da abin da yan ƙasa ke kauna."
A wani labarin kuma Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar
Kotu ta ɗage sauraron karar tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muazu Magaji saboda ta yi karo da shari'ar Sheikh Abduljabbar.
A halin yanzun an ɗage ta Ɗan sarauniya zuwa 4 ga watan Fabrairu, 2022, yayin ta Malam Abduljabbar zata wakana 3 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng