Da duminsa: IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito

Da duminsa: IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana goyon bayan sa ga Bukola Saraki
  • Wakilan Saraki sun ziyarci IBB a gidansa da ke Minna inda suke barar goyon baya yayin da Saraki ya zabura zai fito takarar shugabancin kasa
  • IBB ya bayyana cewa babu shakka Saraki matashi ne mai jini a jika da ya dace da shugabancin Najeriya kuma ya na goyon baya

Babu shakka labari ne mai dadi ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki saboda tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa ga burinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Janar Babangida ya yi martani ne kan bukatar da wakilan Abubakar Bukola Saraki da suka samu jagorancin shugaban kungiyar kamfen din sa, Farfesa Hagher Iorwuese da darakta janar, Osaro Onaiwu wadanda suka je har gidan IBB da ke Minna domin neman goyon baya.

Kara karanta wannan

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Da duminsa: IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito
Da duminsa: IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Babangida wanda ya kasa boye kaunarsa ga Saraki, ya kasa rufe baki don kai tsaye ya ce Saraki tamkar bindigar yaki ce mai harba kanta, a takaice hakan ne kwatancen Saraki, Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda yace, 'yan takara da yawa sun ziyarcesa kuma za su cigaba da zuwa. Amma matashi kamar Saraki wanda ya san kan kasar nan shi ne ya fi dacewa da mulkin kasar nan.

"Na ji dadin samun mutane kamar ku da suka san ma'anar me shugabancin Najeriya ya ke nufi. An rasa wannan ma'anar. Na ji dadi da aka gano wanda zai iya aikin. Mahaifinsa makusanci na ne sosai," yace.

Babangida, wanda aka fi kira da IBB ya jinjinawa kishin kasa na Saraki a matsayinsa na shugaban majalisa na takwas inda yace:

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

"Kokarin Saraki ne ya tseratar da kasar nan har ta tsallake ba ta fada cikin rikici ba. Da ba don shi ba, da Allah kadai ya san abinda zai faru. Hazakarsa ce ta tseratar da kasar nan, don haka shi ne ya fi dacewa da Najeriya.
"Amma kuma akwai jan aiki a gabanmu ta yadda za mu shawo kan 'yan Najeriya har su yadda da hakan. Kun samo wanda ya dace da shugabancin kasar nan. Muna bukatar shugaban da zai duba banbancinmu kuma ya yi amfani da shi yadda ya dace.
"Ba mu yi amfani da banbancinmu ba yadda ya ce, na yadda cewa Saraki ya na jini a jika ta yadda zai iya dawo da sunan kasar nan. Na yi masa addu'a kuma ya na goyon bayan na daari bisa dari."

IBB: Yadda Abacha ya yaudari ƴan gwagwarmaya da fitattun ƴan ƙasa, ya haye mulki

A wani labari na daban, Janar Sani Abacha, wanda ya mulki kasar nan daga 1993 har zuwa rasuwarsa a 1998, ya yaudari 'yan siyasa kafin ya dare mulki, kamar yadda tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda aka fi sani da IBB ya sanar.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

A wata tattaunawa da Trust TV ta yi da IBB, ya yi magana kan yadda Abacha ya yi musu wayau kuma ya dare madafun iko.

Abacha, wanda ya kwatanta da abokinsa nagari, ya yi aiki a matsayin shugaban sojojin kasa a mulkin Babangida kuma daga bisani aka nada shi ministan tsaro a 1990.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng