Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana kansa a matsayin wanda ya cancanci gadar kujerar shugaban kasa a 2023
  • Wike ya ce yana da gogewa da kwarewar da ake bukata daga wajen duk wanda zai shugabanci kasar
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa baya tunanin akwai wani mutum da ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya sama da shi.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, a yayin wata hira a shirin Channels TV na Politic Today.

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023
Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023 Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Yace duba ga shaidar da ya samu a matsayin minista da kuma gwamnan jiha mai arzikin mai, yana da gogewar da ake bukata don shugabantar kasar.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Channels TV ta nakalto yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ga mutum irina, gwamna kuma minista, bana ma ganin akwai wani mutum da zai fada mani cewa ya fi ni cancanta, bana tunanin hakan zai yiwu ma.
“Da ace yau ina son tsayawa takarar Shugaban kasa, wane irin cancanta kuke ganin bani da shi? Me yasa kuke ganin ba zan iya samar da ingantaccen shugabanci da ya dace don Najeriya ta ci gaba ba?
"Bai dace kowani mutum ya ce 'takara ta itace takara mafi kyau ba. Ba na tunanin haka. Abin da nake wa'azi kawai shi ne cewa ya kamata mutane su yi magana a kan batutuwa. Najeriya na da matsala. Idan sun ba ku dama, me za ku yi don ganin ‘yan Najeriya sun amfana?”

Baya ga babban zaben 2023, Gwamna Wike ya kuma yi magana kan ayyukan gwamnatin da ta shige a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Ya tuna cewa a lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015, babu wata takardar mika mulki daga magabacinsa kan ainahin halin da lamura ke ciki a Rivers.

Takara a 2023: Kungiyar CAN ta yi watsi da Yahaya Bello, ta yi karin bayani a kansa

A wani labarin kuma, kungiyar Kiristocin Najeriya a jihohin arewa 19 da Abuja ta yi watsi da rahotannin cewa ta marawa takarar shugaban kasa na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi baya a zaben 2023.

CAN ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar bayan wani gagarumin taro da ta gudanar a otal din Excel da ke Abuja, PM News ta rahoto.

Jami'in hulda da jama'a na kungiyar CAN a jihohin arewa da Abuja, Chaplain Jechonia Gilbert, ya ce kungiyar bata taba tsayar da wani mutum don darewa wata kujerar shugabanci a tarihin zabe a Najeriya kuma ba za ta aikata hakan ba a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng