Shugaban kasa a 2023: Ministan Buhari ya bayyana matsayinsa kan tsayawa takarar kujerar
- Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Sanata Chris Ngige, ya bayyana matsayinsa a kan neman takarar shugaban kasa a babban zaben 2023
- Ngige ya ce a yanzu haka yana kan tuntubar shugabannin siyasar kasar kan kudirinsa na yin takarar
- Sai dai ya ce zai sanar da hukuncin da ya yanke zuwa lokacin bikin Ista
Anambra - Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Sanata Chris Ngige, ya ce yana kan tattaunawa da shugabannin siyasa kuma zai ayyana aniyarsa a kan zaben shugaban kasa na 2023 zuwa lokacin bikin Ista.
Ministan ya bayyana hakan ne a ofishin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya da ke Awka a karshen mako a lokacin da ya ke bayar da tallafi ga mambobin jam’iyyar All Progressives Congress a jihar.
Ngige ya ce:
"Mun fara tattaunawar siyasa kuma. Dan Allah, ku bani zuwa lokacin bikin Ista inda za mu sake taruwa irin haka domin tattauna bukatunku.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Har yanzu ina tuntubar shugabannin siyasa a kasar kan bukatar ku, zuwa lokacin na yanke hukunci, na san yancina ne na yanke hukunci a kan haka. Zan zartar da irin wannan hukuncin a lokacin da ya dace."
Punch ta kuma rahoto cewa wata kungiyar matan Anambra karkashin jagorancin Nancy Okafor ta bukaci Ngige ya tsaya takarar shugaban kasa, inda ta kara da cewa shi ne mutumin da ya dace ya nemi kujerar daga yankin Kudu maso Gabas.
Okafor ta ce:
"Ba ma so mu jira watanni uku kafin kua yanke shawarar ko za ka yi takara ko a'a, muna ba ka umarnin neman wannan matsayi."
Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP
A gefe guda, mun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, na kira ga a bari yankin arewacin Najeriya ya ci gaba da rike mulki a 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya hau karagar mulki a 2015 zai kammala wa'adinsa na shekaru takwas a 2023, lamarin da ya haifar da kace-nace a kasar game da yankin da ya kamata ya samar da shugaban kasa na gaba.
Koda dai manyan jam'iyyun siyasar kasar na APC da PDP ba su riga sun mika tikitin shugaban kasa ga kowani yanki ba, akwai kiraye-kiraye da ake ta yi kan a mika shugabanci ga kudu.
Asali: Legit.ng