Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ya fada wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubukar ya bar neman kujerar shugabancin kasa saboda ya tsufa da yawa kuma a gajiye yake da daukar ragamar Najeriya.
Ya fadi hakan ne a wani jawabi da yayi yayin amsar rahoton kwamitin tuntuba da ya samar na burin sa na tsayawa takarar shugaban kasa wanda ya gudana a ranar Juma'a a tsohon dakin taron Banquet a gidan Gwamnatin Bauchi.
Sunday Punch ta ruwaito yadda kwamiti karkashin jagoranci Adamu Gumba, wanda aka kaddamar a 15 ga Agusta, 2021, bayan ziyartar jihohin arewa 16 inda ta yi hulda da masu rike da mukamai daban-daban a wadannan jihohin.
Muhammad ya ce:
"Na san cewa ko a Bauchi, mutane sun kasu kashi-kashi, yayana, Bala Hadith, ya samu karfin guiwar fadamin cewa mutanen Bauchi basaso inje tsakiyi kuma na gode masa. Wannan saboda ra'ayin mutanen Bauchi ne wanda shi ne yabawa abun da muke yi tare. Bauchi za ta fi haka idan ina tsakiya.
"Amma maganar gaskiya, ya kamata mu kula da duka biyun (Bauchi da yakin neman kujerar shugaban kasa). Na fada wa kanina da abokin tafiya na (mataimakin gwamnan) kada yayi farin cikin tura ni gaba dan ya maye gurbin kujerar gwamna, zan iya hada biyun tare.
"Daya daga cikin 'yan uwa na, dan siyasa mai kwazo, Matawallen Sokoto (Aminu Tambuwal) yayi hakan a baya, saboda haka muma zamu jaraba.
"Babu bukatar mu zama masu son kan mu; tabbas, shugabanci na ba zai janyoo rabuwar kawuna ba. Kamar yadda ku ke gani a lokaci daya yaya na, Malam Adamu ya na kaiwa da komowa, mun gayyaci dattijon kasar mu, daya daga cikin wadanda ake matukar ganin girman su, Wazirin Adamawa (Atiku Abubakar), mun sanya wa wani titi sunan shi domin karrama shi."
Punch ta ruwaito cewa, ya kara da cewa:
"Mun gayyace shi Bauchi kuma mun zanta inda na fadawa masa cewa a wannan wasan, na san shi ne babba, ya cancanta matuka amma saboda shekarun sa da gajiyawar sa yayi wahala sosai da Najeriya, ya bar kanin sa ya zama makwafin sa bawai ya ce zai hau kujerar haka nan ba. Amma idan yan Najeriya shi suka ga ya dace, zan goya masa baya.
"Ba ina neman mulki ido rufe ba ne, amma ina so ya san cewa 'yan Najeriya suna matukar son sa. Kuma duk abin da yake so, zan yi masa, wannan shi ne yarjejerniyar mu, ya na matukar ganin girma na."
Tsohon ministan babban birnin tarayya ya ce 'yan Najeriya sun gane gaskiya kuma suna cikin kangin talauci yayin da zabe ya zamo babban matsalar kasar.
"Muna fuskantar tsananin rashin tsaro, muna fama da matsanancin talauci duk da mutane sun ankare, gwamnati ba ta taba zama kamar haka ba a da, ko sama a daburce ta ke saboda yadda ake tafiyar da mulkin ba tsari. Sannan a yau, ga wasu daga cikin mu da suka sani, an horar da mu a wannan aikin a matsayin masu goyon bayan bogi.
"Duk masu takarar kujerar shugaban kasa daga kowanne bangarori sun cancanta matuka, saboda haka ya rage garemu mu tattauna da juna. A wannan lokacin, ya kamata mu mayar da hankali da hada kawunan mu da neman habaka tattalin arzirkin kasa."
"Ba wai ya zama kungiyar Bala Mohammed kadai ba, za mu canza labarin, kuma za mu tabbatar mun nemo mutanen kirki da kuma mutanen da za su dawo da kananan mazabu su aje wani abu.
"Ba irin mutanen da muke da su da suke zaune a Abuja, ba mu bukatar su. Dole mu canza gwamnati, zabe, tsari da yanayin mulki, wannan shi ne yadda muke bukatar shi.
"Ina farin cikin ganin mutane da yawa suna shiga PDP saboda nan ne fatan mu yake. Ya kamata mu shigo cikin siyasa tare da fahimtar hakkin mutane," a cewar shi.
Asali: Legit.ng