Kungiyoyin mata sama da 600 sun mamaye titunan Abuja, sun goyi bayan gwamna ya gaji Buhari a 2023

Kungiyoyin mata sama da 600 sun mamaye titunan Abuja, sun goyi bayan gwamna ya gaji Buhari a 2023

  • Kungiyoyin mata daban-daban sama da 600 sun gudanar da tattaki domin nuna goyon bayan su ga takarar gwamna Yahaya Bello a 2023
  • Matan sun bayyana cewa Bello ya cancanci ya ɗora daga inda Buhari ya tsaya kuma yana tafiya da mata a mulkinsa
  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, na ɗaya daga cikin waɗan da suka ayyana takarar shugaban ƙasa karkashin APC

Abuja - Punch ta rahoto cewa akalla ƙungiyoyin mata 600 suka tattaru a Abuja ranar Talata, domin nuna goyan baya ga takarar gwamna Yahaya Bello na Kogi a zaɓen 2023.

Ƙungiyoyin sun fito daga shiyyoyin Najeriya shida, kungiyoyi masu zaman kansu, na al'umma, Addini da kuma manyan ƙungiyoyi da suƙa shahara.

Matan ƙaraƙashin babbar kungiyarsu ta masoyan Yahaya Bello 'Women United for Yahaya Bello,' sun gudanar da tattaki mai taken, "mata miliyan ɗaya su yi tattaki saboda Yahaya Bello."

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello
Kungiyoyin mata sama da 600 sun mamaye titunan Abuja, sun goyi bayan gwamna ya gaji Buhari a 2023 Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Matan sun bayyana cewa a shirye suke su yi amfani da duk wani ƙarfin su wajen tallafa wa takarar Yahaya Bello, kuma a cewarsu siyasar bani gishiri in baka manda ta ƙare a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalaman da matan suka faɗa a wurin gangamin

Shugabar ƙungiyar mata yan kasuwa, Vera Ndanusa, tace wannan dandazon matan da suka yi tattaki, alama ce dake nuna, "Duk wanda ya taimaki mace, zai girbi amfani a lokuta da dama."

A cewarta, taimaka wa mata su dogara da kan su, shi yafi dacewa gwamnatin Najeriya ta tasa a gaba kuma ta ba shi fifiko, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Jaruma a masana'antar Nollywood, Binta Ayo-Mogaji, ita ta jagoranci abokan sana'arta da suka haɗa da, Ayo Adesanya, Dupe Jaiyesinmi, Rose Odika da sauran su zuwa wajen taron matan.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku, zasu koma APC

A jawabinta ta yi nuni da kyawawan kalaman da mataimakin shugaban ƙasar Liberia, Jewel Taylor, ya yi a kan gwamna Yahaya Bello. a cewarta su kaɗai sun isa misali.

Shugabar ƙungiyar mata, WUYABEL, ta duniya, Dakta Hannatu Adeeko, ta ce tana sha'awar manyan ayyukan da Gwamna Bello, ya gwangwaje mutanen Kogi da su.

Adeeko, wacce ta taso tun daga Amurka zuwa Najeriya saboda tattakin, ta ce mata sun samu manyan gurabe a gwamnatin jihar karkashin gwamna Bello.

A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi dake Arewa ya tarbi dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jiharsa

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya karbi sabbin mambobin PDP da suka sauya sheka daga APC a fadar gwamnatinsa.

Dandazon mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a yankin Awalah dake cikin kwaryar birnin Bauchi ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262