Sanusi ya yi wa Hadimin El-Rufai mugun baki, ya bi shi saboda ya kira shi tsohon Sarki a taro
- Muhammadu Sanusi II ya ja kunnen Sani Dattijo a wajen taron KADIVEST6.0 a Kaduna
- Tsohon Sarkin ya yi wa babban hadimin baki cewa shi ma zai sauka daga kan kujerarsa
- Makonni da yin hakan ne aka sauke Dattijo daga shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati
Kaduna - Khalifa Muhammad Sanusi II ya halarci wani taron kwadaito da masu hannun jari da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya a watan Satumba.
A wajen wannan taro, shugaban ma’aikatan fadar gwamna, Muhammad Sani Dattijo ya yi jawabi, inda ya kira Muhammad Sanusi II da tsohon Sarkin Kano.
Mai martaba Sanusi II bai ji dadin yadda aka kira shi da tsohon Sarkin Kano ba, ya nuna sam babu wani abu mai kama da tsohon Sarki a sarautar gargajiya.
Wannan ya sa Sarkin da aka tunbuke a 2019 ya gargadi Muhammad Sani Dattijo, har ya kira shi da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati.
Makonni kusan uku da yin wannan magana, sai ga shi Malam Muhammad Sani Dattijo ya rasa mukaminsa a wani sauyi da Gwamna El-Rufai ya yi jiya.
Malam Nasir El-Rufai ya bada sanarwar cire Dattijo daga kujerar da yake kai, kamar yadda amininsa, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi hasashe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da Sanusi II ya fada
“Da na saurari tsare-tsaren da kuma na ji maganar (Dattijo), zan kira shi tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamna, daga baya za ku fahimci dalili.”
“Nan gaba ka da ka kira ni tsohon Sarki, babu wani abu mai kama da haka.” – Sanusi II
Malam Muhammad Sani Dattijo
Mai girma gwamna El-Rufai ya maida Malam Dattijo a kan mukaminsa da ya bari a 2019. Dama can shi ne kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Daga baya sai aka ji an nada matashin a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati. Dattijo, wanda ya na cikin manyan na hannun daman gwamna.
Daga baya sai aka ji an nada matashin a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati. Kafin 2015, Dattijo ya yi da shugaban majalisar dinkin Duniya.
2023: Hasashen Fasto Ayodele
Limamin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Ayodele ya ba Gwamnan Ebonyi, David Umahi shawara ya koma PDP, yace zai yi nadamar shiga APC.
An ji Ayodele yana cewa gwamna David Umahi da Ben Ayade za su gamu da takaici a 2023.. Faston yace sai Umahi ya yi da-na-sanin shiga APC a zaben 2023
Asali: Legit.ng