Jerin 'Yan siyasa 4 da suka ziyarci tsohon shugaban kasa IBB domin kama kafar 2023
- Har gobe duk ‘dan siyasan da ya kai ‘dan siyasa a Najeriya, yana zuwa gaban Ibrahim Badamasi Babangida
- Masu neman kujerar shugaban kasa su kan ziyarci Janar Ibrahim Babangida domin a tofa masu albarka
- Ko a kwanan nan, Bola Tinubu ya kai ziyara zuwa jihar Neja, bai dawo ba sai da ya gana da Babangida
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin fitattun 'yan siyasan da aka gani a gidan IBB a 'yan watannin bayan nan:
1. Orji Uzor Kalu - Agusta 2020
Tun a Agustan 2020, Sanata Orji Uzor Kalu ya ziyarci garin Minna, jihar Neja. A lokacin ya je har gidan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Bayan nan an ji cewa Orji Uzor Kalu zai ziyarci gidan Abdulsalami Abubakar da wajen gwamna Abubakar Sani Bello da Mai martaba Sarkin Lapai, Etsu Umaru Bago.
Sai dai watakila ziyarar ba ta da nasaba da 2023 domin an yi ta ne tun kafin a fara shirin zabe.
2. Atiku Abubakar – Oktoba 2020
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A watan Oktoban 2020, an ji labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai ziyara Jihar Neja inda ya hadu da tsohon Shugaban kasa, Babangida.
Atiku ya sa kafa a filin jirgin saman jihar Neja da rana tare da ‘yan tawagarsa, daga nan suka wuce gidan Babangida wanda ya yi mulki daga 1985 zuwa 1992.
Ana zargin tattaunawar ta su ba za ta rasa alaka da zaben shugaban kasa da za ayi a badi ba.
3. Anyim Pius Anyim – Disamban 2021
A ranar 2 ga watan Disamban 2021, Ibrahim Badamasi Babangida ya karbi bakuncin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim a gidansa a Minna.
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Anyim Pius Anyim yana cikin wadanda suke neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.
Anyim ya gana da Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar kan shirinsa na neman mulki.
4. Bola Tinubu – Junairun 2022
A ranar 20 ga watan Junairu 2022, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara zuwa jihar Neja, inda shi ma ya je har gida ya gaida Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Hakan na zuwa ne a lokacin da jagoran na jam’iyyar APC watau Bola Ahmed Tinubu yake cigaba da fafutukar samun takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa.
Tinubu ya tabbatar da cewa ya zo wajen tsohon shugaban kasar ne domin ya nemi albarkarsa.
Sam Ohuabunwa zai yi takara
Kwanakin baya aka ji cewa Sam Ohuabunwa ya sanar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu shirin da yake yi na fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
Ohuabunwa yana cikin wadanda suka fito tun yanzu suka bada sanarawar cewa za su nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta kasar.
Asali: Legit.ng