2023: Kalu ya ziyarci IBB, ya ce babu tsarin karba-karba a APC
- Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya ce babu tsarin karba-karba a kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC
- Sanata Kalu, bulaliyar majalisar dattijai, ya ce tikitin takarar shugaban kasa na APC a shekarar 2023 na mai rabo ne
- A cewar Kalu, gwamnati ta gaza shawo kan matsalar tsaro a Najeriya saboda akwai ma su yi ma ta zagon kasa a cikin gida
Bulaliyar majalisar dattijai kuma tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya ziyarci tsohon shugagaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Kalu ya bayyana cewa babu tsarin karba-karba a batun neman tikitin kujerar takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a shekarar 2023 tare da fadin cewa; "mukami ne a kasuwa, duk mai so zai iya nuna bukatarsa."
Tsohon gwamnan ya yi wadannan kalamai ne yayin da ya ke magana da manema labarai bayan kammala ganawar sirri da IBB a gidansa da ke Minna.
Ya kara da cewa batun karba-karba tsarin jam'iyya ne kuma babu hakan a jam'iyyar APC, lamarin da yasa tikitin takarar shugaban kasa na APC a shekarar 2023 ya zama na mai rabo.
"Duk mai sha'awa zai iya tsayawa takarar kujerar shugaban kasa, ba a mika takara zuwa wani bangare na kasa ba, sannan babu tsarin karba-karba a kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC, a saboda haka duk mai so zai iya fitowa a buga da shi," a cewarsa.
DUBA WANNAN: Sunaye: Buhari ya rantsar da kwamitin tuntuba na jam'iyyar APC
Da ya ke magana a kan batun tsaro, Kalu ya bayyana cewa akwai ma su cin dundinyar gwamnati a kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro, lamarin da ya sa har yanzu ta gaza samun galaba a kan matsalar.
A cewar tsohon gwamnan, zagon kasa ne kadai ya sa har yanzu duk dabarun da gwamnati ta bullo dasu su ka ki yin tasiri a yaki da matsalar rashin tsaro a fadin kasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng