Da Dumi-Dumi: Gwamnan Arewa ya goyi bayan Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa a 2023
- Gwamna Abubakar Sani Bello, na jihar Neja ya nuna amincewarsa da kudirin jagoran APC, Bola Tinubu, na maye gurbin Buhari a 2023
- Gwamnan ya bayyana cewa Tinubu ya kafa tushe mai kyau a jihar Legas, yan Najeriya za su so hakan ta faru a Najeriya baki ɗaya
- Yace tubalin da Tinubu ya gina a Legas, ya sa jihar ta zama tankar wata ƙasa ce mai gashin kanta a cikin ƙasar nan
Niger - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya goyi bayan kudurin jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya maye gurbin shugaba Buhari a zaben 2023.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da Tinubu ya kai masa ziyarar jaje kan ayyukan ta'addancin yan bindiga a jihar Neja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Gwamnan yace cigaba da ɗaukakar da yan Najeriya ke ganin jihar Legas ta samu, duk sakamakon tubalin da Tinubu ya gina ne a lokacin da yake gwamna.
Ya kuma ƙara da cewa matukar tsohon gwamnan zai iya gyara jihar Legas, to babu tantama zai iya jagorantar Najeriya baki ɗaya.
Wace nasara Tinubu ya samu a jihar Legas?
Gwamnan yace tubalin da Tinubu ya kafa a jihar Legas, shi ne musabbabin da ya sa jihar ta yi zarra a bangaren kasuwanci a faɗin Najeriya.
Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa, Abubakar Bello, yace:
"Allah mai girma da ɗaukaka cikin ikonsa ya ba Bola Tinubu damar kafa tubali mai ƙarko a jihar Legas, wanda sakamakon shi ne muke gani a yanzu."
"Jihar Legas ƙasa ce a cikin ƙasar nan, kuma mun shaida irin kyakkyawan jagorancin da ka shuka a jihar yau, mun ƙagara mu ga lokacin da zaka maimata haka a matakin ƙasa gobe."
A wani labarin na daban kuma Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023
Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu , ya fara bayyana wa yan Najeriya manufofinsa bayan ɗarewa karagar mulki a 2023.
A cewarsa, da zaran ya ɗare karagar mulki a 2023, yan Najeriya sun gama kuka kan biyan kuɗin WAEC , zai biya wa kowane ɗalibi a Najeriya.
Asali: Legit.ng