2023: Wani gwamnan APC daga kudu ya nuna sha'awar gadon kujerar Buhari, ya bada sharaɗi
- Gabanin zaben 2023, Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross Rivers ya nuna sha'awarsa na fitowa takarar shugaban kasa
- Amma, gwamnan ya ce zai fito takarar ne kadai idan jam'iyyarsa, APC mai mulkin kasa, ta ga cewa ya cancanta ya tsaya takarar
- Ayade ya ce zai mara wa jam'iyyar baya ko da kuwa ba shine aka bawa tikitin takarar shugaban kasa ba a shekarar ta 2023
Jihar Cross River - Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade ya ce, zai fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023 idan jam'iyyarsa ta All Progressives Congress, APC, ta tsayar da shi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, a lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri a Channels TV, The Cable ta ruwaito.
Da aka masa tambaya ko zai yi takarar shugabancin kasa a 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar APC, gwamnan ya ce ya kamata jam'iyyarsa ta yi amfani da tsarin karba-karba.
Amma da aka saka masa tambaya kan batun takarar, Gwamna Ayade ya ce zai fito takarar idan jam'iyyarsa ta ga cewa ya 'cancanta'.
Ya ce:
"Ina tunanin ya dace jam'iyyar ta dauki matakin bisa la'akari da tsarin karba-karba tsakanin yankunan.
"Zan iya cewa, eh da a'a. Idan jam'iyyar mu ta APC taga cewa na dace kuma na cancanta, eh. Idan kuma jam'iyyar ta ga cewa akwai wanda ya fi ni dacewa bisa tsarin karba-karban, tabbas zan goyi bayan matakin jam'iyyar.
"Ni mutum ne mai bin dokoki; ina tare da jam'iyya. Ban taba zama mara bin tsari ba. Ina aiki ne tare da yadda aka tsara abubuwa."
'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare
A wani labarin, Babban dan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, Mohammed, ya ziyarci Sanata Orji Uzor Kalu, a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu.
Duk da cewa Kalu bai bayyana ainihin abin da suka tattauna ba, ya ce ya karfafa wa Mohammad gwiwa da cewa ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Tsohon gwamnan na Jihar Abia ya cigaba da cewa yana fatan bakon da ya kai masa ziyara zai dauki shawarar da ya bashi.
Asali: Legit.ng