Shugabanci a 2023: 'Yan kamfen din Atiku sun yi watsi dashi sun kama wani dan takara
- Wata kungiyar goyon baya ga Atiku Abubakar ta bayyana yadda ta koma tsagin Bukola Saraki ba tare da juya baya ba
- Shugaban kungiyar ya ce Atiku bai tsinana musu komai ba, don haka sun yi watsi da batun tsayawarsa takarar shugaban kasa
- Sun ce Saraki ne ya cancanci gadan kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023, don haka za su saya masa fom din takara
Birnin Tarayya, Abuja - Wata kungiyar yakin zaben Atiku Abubakar mai suna Atiku Ambassadors, ta yi watsi dashi, ta kuduri aniyar marawa tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki baya, a zaben shugaban kasa na 2023.
Shugaban kungiyar Mufra Jibrin ne ya bayyana matsayar kungiyar lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa ga kodinetan kungiyar ‘Saraki Is Coming Door To Door’ Umar Faringado Kazaure a gidansa da ke Abuja, Daily Nigerian ta rahoto.
Jibrin, dan garin Kafanchan kuma dan kasuwa, ya ce a yanzu tsohuwar kungiyarsa ta dawo daga rakiyar Atiku ta hade da kungiyar ‘Saraki Is Coming Door To Door’.
Manufar yin hakan a cewarsa, shi ne don tabbatar da aniyar Dakta Saraki ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A hirarsa da manema labarai, Jibrin ya ce Atiku bai tsinanawa tsohuwar kungiyar komai ba tun daga zaben 2016 har zuwa 2019, inda ya kara da cewa kungiyar ta kashewa Atiku kudi da yawa.
A cewarsa:
"Tun daga lokacin, mun fahimci cewa bai cancanci a goyi bayan Atiku ba. Haka kuma akwai lokaci ga komai a rayuwa. Yanzu lokaci ne na matashi, mai kuzari kuma gogaggen dan takara a kamar Saraki, ya zama shugaban Najeriya na gaba a 2023.
“Bisa la’akari da halin da al’ummar kasar ke ciki, Najeriya na bukatar Saraki ya juya al’amura. Kwarewarsa da kishin kasa ba a taba shakkarsa ba domin duk mun ga yadda ya jagoranci majalisar dattawa ta 8 da ma majalisar dokoki.
"Ya sanya Majalisar Dokoki ta kasa ta yi amfani kuma za mu iya ganin bambanci a yau.
“Don haka za mu fara nuna goyon bayanmu ta hanyar fara sayen fom din tsayawa takara ga Dakta Bukola Saraki domin ya tsaya mana takarar shugaban kasa.”
Da yake mayar da martani, Mista Faringado ya yi maraba da batun, inda ya ce masu tunani iri daya musamman matasan Najeriya irin su na da matukar muhimmanci wajen ceto kasar nan daga kalubalen da take fuskanta.
EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC
Kawo yanzu akwai ‘ya ‘yan APC da ke harin kujerar da Adams Oshiomhole ya bari a 2020. Punch ta ce ana zargin wasu daga cikinsu da rashin gaskiya.
Jaridar ta kawo jerin wasu masu neman kujerar shugaban jam’iyya da zargin da ke kan wuyansu.
Daga cikinsu, akwai Abdulaziz Yari, Danjuma Goje da dai sauran 'yan siyasa.
A wani labarin, gamayyar matasa karkashin kungiyar North-East Young Technocrats For Good Governance ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ahmadu Adamu Mu'azu, ya fito takarar shugaban kasa a 2023.
Shugaban kungiyar na kasa, Dr Mohammed Abdullahi da Sakatare, Mr Solomon David cikin wata takarda da suka fitar a Bauchi sun ce tsohon gwamnan yana da gaskiya da rikon amana da zai iya yakar rashawa da rashin adalci a kasar, Vanguard ta ruwaito.
A cikin takardar, sun ce Mu'azu zai magance wariya, rashin tsaro, talauci, kabilanci da sauran abubuwan yau da kullum da ke adabar kasar.
Asali: Legit.ng