EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

  • FCT, Abuja - Tun a watan Yunin shekarar 2020 aka nada gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC
  • An sa ran cewa gwamna Mala Buni zai shirya zaben shugabanni na kasa, inda za a samu ‘yan majalisar da za su dare mukaman NWC na jam’iyya
  • Bayan kusan shekaru biyu a kan mulki, har yanzu ba a kai ga shirya wannan zaben ba, an kuma kara wa’adin kwamitin rikon kwaryan sau uku

Kawo yanzu akwai ‘ya ‘yan APC da ke harin kujerar da Adams Oshiomhole ya bari a 2020. Punch ta ce ana zargin wasu daga cikinsu da rashin gaskiya.

Jaridar ta kawo jerin wasu masu neman kujerar shugaban jam’iyya da zargin da ke kan wuyansu:

Kara karanta wannan

COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a shekara 2

Abdul’Aziz Yari

EFCC ta na zargin tsohon gwamnan Zamfara, Abdul’Aziz Yari da laifin karkatar da N19,439,225,871.11 daga asusun biyan bashin Paris Club.

Sannan EFCC ta je kotu tana neman iko da wasu N500m da $500,000 da ta karbe a hannun Yari

Tanko Al-Makura

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi ma Tanko Al-Makura wanda ya yi gwamna a jihar Nasarawa bai tsira ba. A shekarar da ta wuce, EFCC ta kira shi hedikwatarta, tayi masa tamabayoyi.

Masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC
Abdul’Aziz Yari, Tanko Al-Makura da Ali Modu Sheriff Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ali Modu Sheriff

EFCC ta dade ta na tuhumar Ali Modu Sheriff da laifuffuka da ya aikata a baya. Sannan Ana zarginsa da karbar N40m a hannun Diezani Alsion-Madueke

Danjuma Goje

Sanata Danjuma Goje ya yi gwamna a Gombe daga 2003 zuwa 2011. Tun bayan saukarsa EFCC ta ke nemansa, daga baya sai aka ji an janye zargin da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

George Akume

Ya na gama mulki a 2007 aka ji EFCC ta na neman George Akume. An taba tsare Akume bisa zargin ya saci biliyoyi kafin Farida Waziri ta bada belinsa.

Isa Yuguda

Isa Yuguda yana neman kujerar shugaban APC na kasa. Shi ma ana zargin ya batar da N6.181b da sunan tsaro da yake gwamna, amma EFCC ba ta tabo shafinsa ba.

Sabon shugaban APC

Kun ji akwai alamu da ke nuna Arewa maso tsakiya za su fito da sabon shugaban jam’iyyar na kasa da zai gaji Mai Mala Buni, kuma za a ba Ibo Sakatare.

Wannan mataki da za a dauka zai wargaza lissafa ‘yan siyasa irinsu tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari da Sanata Ali Modu Sheriff da suka ci buri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng