Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

  • Rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulki reshen jihar Zamfara ya dauka sabon salo inda ake amfani da 'yan daba wurin kai wa abokan adawa farmaki
  • Tsagin Yari ya ce abun tashin hankali ne yadda 'yan siyasa ke daukar nauyin 'yan daba suna kai wa jama'a farmaki saboda wasu banbanci
  • Sai dai tsagin gwamna Matawalle ta bakin sakataren yada labaran su, sun ce zantuka ne marasa tushe daga wadanda aka daina yayin su a siyasa

Zamfara - Rikicin cikin gida na cigaba da rincabewa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Zamfara inda sabon salo ya kunno kai a cikin tsagi daban-daban na jam'iyyar ta yadda ake daukar nauyin kai farmaki da 'yan daba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsagin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya nuna firgici da tashin hankali a jihar inda suke zargin za a mayar da jam'iyyar filin daga inda 'yan daba ke baje-kolin su.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Zamfara APC: Rikici ya jagwale tsakanin tsagin Marafa da Matawalle, ana amfani da 'yan daba
Zamfara APC: Rikici ya jagwale tsakanin tsagin Marafa da Matawalle, ana amfani da 'yan daba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban tsagin, Lawal M. Liman, wanda ya yi wannan hasashen, ya bayyana cewa, farmakin kwanan nan da aka kai wa shugaban fannin yada labarai na kafafen sada zumuntan Sanata Kabiru Gwarba Marafa na jam'iyyar, Malam Shamsu Shehu datsakar rana ya zama abun tashin hankali ga duk mai san zaman lafiya da kiyaye doka a jihar.

Hakazalika, tsagin Sanata Kabiru Marafa ya kushe wannan farmakin inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tsamo miyagun ko kuma dole su dauka matakin da ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren yada labarai na Marafa, Bello Bakyasuwa, a wata takarda da ya fitar ya ce ba za su kalmashe hannu su zauna suna kallo ana hantarar mambobin su ba.

Sai dai a martaninsu, tsagin Matawalle ta bakin sakataren yada labaran su, Yusuf Idris Gusau, ya ce zargin ba shi da tushe balle makama kuma ya fito ne daga wadanda aka daina yayin su a siyasar Zamfara.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce daga cikin dalilan da suke assasa wutar ta'addanci akwai kyale 'yan bindigar da 'yan ta'adda da ake yi babu wani hukunci.

A cewar gwamnan, sau da yawa ana sakin 'yan bindigan daji ba tare da an yi musu wani hukunci ba, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karba wakilan gwamnatin tarayya yayin da suka je masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai wa wasu yankunan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng