Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan kungiyar gwamnoni ya yi murabus

Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan kungiyar gwamnoni ya yi murabus

  • Daraktan kungiyar gwamnonin APC, Mohammed Salihu Lukman ya hakura da shugabancin kungiyar ya yi murabus
  • Murabus din nasa ya biyo bayan zaman da jam'iyyar ta yi don tattauna batutuwan da suka shafi taron gangaminta
  • A cikin 'yan kwanakin nan ana ta samun rikici a jam'iyyar APC, lamarin da jawo hankalin 'yan siyasa da dama

Abuja - Darakta Janar na kungiyar gwamnonin APC, Mohammed Salihu Lukman, ya mika takardar murabus dinsa ga kungiyar ta PGF.

Murabus din nasa a ranar Litinin ya zo ne sa’o’i 24 bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar APC a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi a daren Lahadi.

Kokarin jin martanin daraktan na PGF bai samu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Jam'iyyar APC ta kara rincabewa
Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan PGF ya yi murabus | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sai dai kuma Leadership ta gano cewa matakin na saukar DG din daga mukaminsa, tare da yin murabus ta yiwu ya zo ne a taron gwamnonin APC da aka ce an samu rarrabuwar kawuna kan makomar Lukman.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya a taron ta nuna cewa gwamnonin sun tattauna matsayar Lukman kan shugabancin jam’iyyar da ya sha suka a kwanakin baya kan kin gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta

Gwamnoni karkashin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) sun shiga taro domin neman matsaya kan gangamin taron jam'iyyar da za a yi.

Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi da ke yankin Asokoro da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Rikici ya na cin jam'iyyar mai mulki tun bayan da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya kasa shirya taron zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

A watan Nuwamban 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan shugabannin jam'iyyar a gidan gwamnati da ke Abuja, inda aka amince kan cewa za a yi zaben sabbin shugabannin jam'iyyar a watan Fabrairu, duk da ba a tsayar da rana ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ku aika duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan yari Lahira, Minista ga Jami'ai

A wani labari na daban, rikici ya na ci gaba da kamari tsakanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aliero wanda hakan zai janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.

Shugabannin jam’iyyar na kasa da jihar sun bayyana wa manema labarai cewa, daga Bagudu har Aliero su na da wanda suke son a tsayar takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Rahotanni sun nuna yadda Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ke so a daura antoni janar, Abubakar Malami a matsayin dan takara, yayin da Alieru wanda ya yi gwamna har sau biyu a jihar, yake son a tsayar da Yahaya Abdullahi, wanda shugaba ne na majalisar dattawa a dan takarar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.