Da duminsa: Ganduje ya ziyarci shugaban APC na tsagin Shekarau, Ahmadu Danzago
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci shugaban APC na jihar Kano, tsagin Shekarau, Ahmadu Danzago
- Duk da shari'ar da suke ta tafkawa a kotu, Ganduje ya je yi wa Danzago ta'aziyyar rasuwar dan uwansa na ranar Asabar
- Sabon hadimin gwamnan a fannin kafafen sada zumunta, Abubakar Ibrahim, ya sanar da cewa gwamnan ya kai ziyara tare masu mukaman siyasa
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Lahadi, ya kai ziyarar ta'aziyya ga shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Ahmadu Danzago, wanda ya karba kujerar a kotu.
Ya kai wa Danzago ziyarar ne sakamakon mutuwar da da yayansa ya yi a ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.
An zabi Danzago a matsayin shugaban APC a jihar a zaben da aka yi na ranar 18 ga watan Oktoba, 2021 wanda tsagin tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau suka yi.
Gwamna Ganduje a ranar ya yi zaben shugaban jam'iyyar a jihar ga mabiyansa wanda hakan ya samar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata wallafar da sabon hadimin Ganduje, Abubakar Ibrahim ya yi a Facebook, ya ce gwamnan ya samu rakiyar Abbas.
Hakazalika, a tawagar gwamnan akwai wasu masu mukaman siyasa a gwamnatinsa, Premium Times ta ruwaito.
Ziyarar ta biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja na ranar Alhamis inda ta yi fatali da bukatu biyu da tsagin Ganduje suka mika na tube Danzago daga shugabancin jam'iyyar a Kano.
Daga hukuncin ranar 30 ga watan Nuwamba da na 17 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, duk tsagin Ganduje aka lallasa.
Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu
A wani labari na daban, daya daga cikin lauyoyin da ke kare bangaren APC din jihar Kano ta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shari’ar da su ke yi ya ce ba su sha kaye a shari’ar da aka yi a kotun Abuja ba.
Yayin tsokaci dangane da rahotannin da ake yadawa a kan shari’ar, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya sanar da Daily Trust cewa mutane sun dinga sauya asalin abinda aka yi a kotu don nuna kamar bangaren Ganduje sun fadi shari’ar ne.
Ya bayyana yadda alkalin kotun, Mai shari'a Hamza Muazu ya ce ba zai ci gaba da sauraron karar ta bangaren Ganduje ba saboda ba shi da hurumin yin hakan, sai dai su daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.
Asali: Legit.ng