Jam'iyyar PDP ta canza ranar babban gangamin taron ta na Arewacin Najeriya

Jam'iyyar PDP ta canza ranar babban gangamin taron ta na Arewacin Najeriya

  • Jam'iyyar Adawa PDP ta saka ranar babban taronta na yankin arewa maso yamma, wanda zata zabi shugabanni
  • Wannan na zuwa ne bayan PDP ta samu nasarar kammala zaɓen shugabanni a matakin ƙasa tun a shekarar 2021 da ta gaba ta
  • PDP ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da kuma mambobinta masu haɗin kai su fara shirye shiryen taron kuma su bi matakan da aka tsara

Abuja - Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta saka ranar babban taron ta na zaɓen shugabanni a yankin arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jam'iyyar ta zaɓi ranar 12 ga watan Fabrairu, na shekarar 2022 da muke ciki, a matsayin ranar taron da aka jima ana jira.

Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP ta canza ranar babban gangamin taron ta na Arewacin Najeriya Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren shirye-shirye na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Honorabul Umar Bature, ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood

A cewar sanarwan, wannan na ɗaya daga cikin batutuwan da kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP ta ƙasa ya amince da su a taron ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Honorabul Bature, ya bayyana cewa za'a gudanar da taron na Arewa maso yamma a Hedkwatar jam'iyyar PDP dake jihar Kaduna.

Haka nan kuma ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da kuma mambobin jam'iyya masu haɗin kai na yankin arewa ta yamma su shirya wa taron.

Kazalika ya roki dukkan masu faɗa aji da mambobin su bi doka sau da kafa yayin gudanar da taron, domin a gudanar da shi lafiya.

Daily Nugerian ta rahoto wani sashin sanarwan na cewa:

"Da wannan muna sanar da baki ɗaya masu ruwa da tsaki da mambobin jam'iyyar mu mai albarka su shirya wa taron."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

A wani labarin na daban kuma Ya'yan tsohon shugaban sojojin Najeriya sun maka kawunsu a gaban kotu kan dukiyar gado

Lauyan 'ya'yan marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa a Najeriya, Janar Luka. N Yusuf, sun gurfanar da kawunsu a gaban kotu a Kaduna.

A takardar shigar da kara mai ɗauke da sakin layi 15, masu shigar da kara sun roki kotu ta taimaka wajen dawo musu da dukiyar mahaifin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262