2023: Ina fuskantar matsin lamba kan cewa in fito takara, in kuma ziyarci Buhari in sanar da shi, Orji Kalu
- Tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu ya bayyana cewa zai sanar da Buhari ƙudirin takararsa a lokacin da ya dace
- Kalu ya ce ya fara fuskantar matsin lamba ne bayan da ragowar masu neman kujerar suka ziyarci Buhari
- Tsohon Gwamnan yace da zarar APC ta bawa yankin Kudu damar fito da ɗan takara, to zai sanar da Buhari
Bulaliyar Majalisar Dattijai, Senata Orji Kalu, ya ce yana fuskantar matsin lamba kan lallai sai ya bayyana ƙudirin takararsa ya kuma kaiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara, kamar yadda mutum biyu masu sha'awar kujerar a APC suka yi.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ziyarci Buhari a gidan gwamnati a Abuja, ranar Litinin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake amsa tambaya daga manema labarai na fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya bayyana cewa ya shaidawa Buhari niyyar sa na yin takarar shugabancin ƙasa kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnan Ebonyi ya sanar da Buhari zai yi takara
Gwamnan Ebonyi, David Umahi, ranar Talata, shima ya kai ziyara ga shugaban ƙasar. Jim kaɗan bayan gama tattaunawar su, gwamnan ya ce ya shaidawa Buhari niyyarsa ta takarar shugabancin ƙasa.
Kalu, wanda tsohon gwamnan Abia ne, wanda ake ganin yana cikin wanda ka iya gadar Buhari, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ranar Laraba, ya ce yana jira ne yaga ko APC zata bawa Kudu damar fitar da ɗan takara.
Ya ce wannan ne zai nuna masa ko zai ziyarci shugaban ƙasar. Kamar yadda yace:
"Yan uwana ƴan Najeriya. Ina fuskantar matsin lamba da roƙo kan in sanar da bukatar yin takarar shugabancin ƙasa kuma in ziyarci shugaban ƙasa kamar yadda yan uwana suka yi jiya."
Ya ƙara da cewa:
"Da zarar jam'iyya ta bawa yankin Kudu damar fitar da ɗan takara, jirgina wanda ya jima yana jira zai sauka fadar Aso Rock in sanar da shugaban ƙasa abin da muka yanke. Allah ya muku albarka."
Asali: Legit.ng