Ta'addanci: Ku gayyaci shugabannin APC su muku bayani, PDP ga hukumomin tsaro
- Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda
- PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015
- Haka nan PDP ta yi zargi cewa jam'iyya mai mulki na fakewa da tattaunawar sulhu, tana taimakawa yan bindiga da kuɗaɗe
Abuja - Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yi kira ga hukumomin tsaro su gayyaci shugabannin APC domin amsa tambayoyi kan zargin alaƙa da yan ta'adda.
Punch ta rahoto cewa PDP na ganin haka ya zama wajibi biyo bayan ayyana yan bindiga da suka addabi arewa a matsayin yan ta'adda da gwamnatin tarayya ta yi.
A cewar PDP, akwai bukatar jagororin APC su yi karin haske, "Bisa rahoton shigo da yan ta'adda cikin ƙasar nan da kuma kyale su, suna aikata ta'addanci kan yan Najeriya."
Wannan zargi na ƙunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na PDP ta ƙasa, Debo Ologunagba, mai taken, "Ta'addanci: Ku gayyaci shugabannin APC su amsa tambayoyi, PDP ga hukumomin tsaro."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tribune ta rahoto Wani sashin sanarwan yace:
"Jam'iyyar mu na rokon hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan ikirarin tsohon mamban APC cewa jam'iyyar ta shigo da yan ta'adda a 2015 domin su taimaka mata wajen murde zaɓe."
"Ya kamata yan Najeriya su san dalilin da ya hana APC da shugabannin ta kawo karshen ayyukan ta'addanci a ƙasar mu tsawon shekaru. Maimakon haka wasu daga ciki sun koma goyon bayan abin da ke faruwa."
Ana amfani da kudin ƙasa - PDP
Bugu da ƙari, jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa APC na amfani da kuɗin al'umma na ƙasa wajen tallafa wa yan ta'adda da sunan tattaunawa.
Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai
"Wani rahoto ya nuna yadda APC ke taimaka wa yan ta'adda da kuɗaɗen gwamnati na al'umma da sunan tattaunawa."
"Bisa haka PDP na rokon hukumomin tsaro su gaggauta fara bincike domin bankado duk masu hannu a ta'addanci kuma su tona asirin shugabannin APC da aka gano suna da hannu."
A wani labarin na daban kuma Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai
Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20.
Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn.
Asali: Legit.ng