Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

  • A wata tattaunawa da aka yi da Babatunde Fashola a watanni biyu da suka gabata, ya sanar da cewa a watan Fabrairu Tinubu zai sanar da burinsa na takara
  • A ranar Litinin, Asiwaju Bola Tinubu, shugaban jam’iyya mai mulki na kasa ya sanar da manema labarai cewa ya fada wa shugaba Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa
  • Hakan bai zama abin mamaki ba saboda dama Tinubu ya dade yana kamfen din kujerar tun kafin ya yi maganar a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock

Wani lokacin, ‘yan siyasa su na shirya komai kafin su sauka daga wani mukami wanda daga bisani sai su yi kamar dama faruwa ya yi ba tare da shirinsu ba.

A ranar Litinin, Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam’iyyar APC, ya sanar da manema labarai cewa ya fada wa shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Martanoni da ra’ayoyin mutanen Facebook game da burin Tinubu na zama Shugaban Najeriya

Sai dai hakan bai ba jama’a mamaki ba saboda yadda Tinubu ya dade yana kamfen din shugabancin kasa tun kafin ya yi maganar a Aso Rock.

Sai dai tambayar da ‘yan Najeriya da dama su ka dinga yi shi ne, “meyasa sai yanzu?”

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu
Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watanni 2 da suka gabata, Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, wanda ya gaji mulkin jihar Legas a 2007, ya bayar da wannan tsokacin.

Yayin wata tattauna da Channels TV ta yi da shi a wani shiri na ‘Hard Copy’, an tambayi Fashola idan yana goyon bayan takarar Tinubu, inda ya amsa da cewa:

“Mun hadu a makon da ta gabata; amma bai sanar da ni cewa zai tsaya takara ba kuma cewa ya yi a wata takarda da ya saki cewa zuwa watan Janairu kowa zai san abinda ake ciki,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

An kara tambayarsa idan ya tambayi Tinubu, inda ya ce bai tambaya ba, kawai na tsaya in ga gudun ruwansa ne.

“A iya sani na babu wanda ya fito ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
“Ba zan bude baki in yi wa wani magana ba. A jira shi ya zo da bakinsa ya yi maganar yi wa kasa aiki.”

Martanoni da ra’ayoyi mutanen Facebook game da burin Tinubu na zama Shugaban Najeriya

A wani labari na daban, shahararren ‘dan jaridar nan wanda yanzu haka yake boye a Birtaniya, Jafar Jafar ya nuna cewa ya na cikin wadanda ba za su marawa Bola Tinubu baya ba.

Jafar Jafar a shafinsa na Facebook ya rubuta “Kowa ya ci ladan kuturu…

Can kuma sai ya fito a mutum ya ce “Ka yi wa mutan Kano laifi. Har yanzu ba mu manta ba. Ni dai ba na yi!”

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng