Martanoni da ra’ayoyin mutanen Facebook game da burin Tinubu na zama Shugaban Najeriya
- Abuja - A ranar Litinin, 10 ga watan Junairu, 2022, jigon APC Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa Duniya cewa zai yi takarar shugabancin kasa
- Legit.ng Hausa ta tattaro ra’ayoyin wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook, inda ake cigaba da tofa albarkaci a kan niyyar babban ‘dan siyasar
- Wasu mutane sun fara nuna cewa sam ba za su marawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya ko da ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ba
Me mutane su ke cewa a Facebook?
Shahararren ‘dan jaridar nan wanda yanzu haka yake boye a Birtaniya, Jafar Jafar ya nuna cewa ya na cikin wadanda ba za su marawa Bola Tinubu baya ba.
Jafar Jafar a shafinsa na Facebook ya rubuta “Kowa ya ci ladan kuturu…”
Can kuma sai ya fito a mutum ya ce “Ka yi wa mutan Kano laifi. Har yanzu ba mu manta ba. Ni dai ba na yi!”
Shi ma Abdullahi Jalo ya ce Tinubu zai zama shugaban kasa a cikin ruwan sanyi, amma ba da kuri’a ta ba.
Musa Haan ya yi fashin baki, ya na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ka manta da abin da ku kayi mana a zaben 2019, wanda Abba ya ci zabe ku ka kwace mana zaben mu?
Ba za muyi Tinibu ba, kuma mu ma lokaci ya zo da za mu rama irin dandana mana bakin cikin da ku kayi.”
- Musa Haan
"Duk kashe mutanen da akeyi a Arewa, Tinubu bai taɓa cewa uffan ba, amma yanzu yana son Ƙuri'ar Marayu da aka bari. Iya shege!"
- Mubarak Anwar
"Burin Tinubu ba zai je ko ina ba!"
- Fadima Ibrahim
"Wai ma waye ze yi wa Tinubu VP (Mataimaki)? Muslimi da Muslimi kenan? Ko ya ya? APC tazo da Bidia mabayyaniya! Amma Allah yayi mana zabin alheri."
- Umar Sheikh Munry
Shi kuma wani Ahmad Sani ya ce:
"Ga ‘Yan takara na nan a jerin wadanda na fi kauna;
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Bola Ahmed Tinubu
Atiku Abubakar"
An kashe 'Yan Arewa ya na Gwamna
“Ya dade Yana cutar da Arewa kuma ba mu manta ba, ya na gwamna ya goyi bayan OPC sukai ta kashe mana mutane a Lagos amma wai yanzu wawayen cikinmu sune suke masa kamfe. Allah wadaran naka ya lalace, akan kudi zasu sayar da mutuncin jama' arsu, bazamu yadda ba…"
- Saidu Danladi
Yau kuma?
Ganin ya fara hangen zama shugaban kasa, irinsu Nura Shittu sun tunawa Bola Tinubu abin da ya fada a shekarun baya na cewa bai yarda cewa Najeriya kasa daya ce ba.
Tinubu zai kai labari?
Dazu kun ji cewa daga cikin wadanda za su kawo Asiwaju Bola Tinubu cikas akwai tsohon yaronsa, Kayode Fayemi da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
A jam’iyyar PDP kuwa, wadanda ake tunanin za su nemi tutar shugabanci sun hada da Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Legit.ng