Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da Bola Tinubu a Aso Villa
- Jagoran jam'iyyar APC ta kasa, Bola Tinubu, ya dira fadar shugaban ƙasa, ya shiga ganawar sirri da shugaba Buhari
- Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugabannin APC ke cigaba da samun sabani game da babban taron jam'iyya na ƙasa
- A makon da ya gabata, gwamnan Filato, Simon Lalong, gwamna Mala Buni na Yobe, sun gana da Buhari kan lamarin taron
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sa labule da jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Tinubu, a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
The Nation ta tattaro cewa babu hakikanin abin da jagororin suke tattaunawa zuwa yanzun da muke haɗ wannan rahoton.
Wannan ganawa na zuwa ne yayin da sabon cece-kuce da sabani ya barke a tsakanin shugabannin jam'iyyar APC wanda ke barazana ga gudanar babban taron jam'iyya na ƙasa.
A rahoton Daily Trust, tace sabanin da ake samu tsakanin shugabannin APC game da saka ranar babban taro na ƙasa, shi ne maƙasudin ganawar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana ganin Bola Tinubu ne a kan gaba cikin masu hangen tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a babban zaɓen 2023.
Gwamnoni sun ziyarci Buhari kan taron
A ranar jumu'a da ta gabata, shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya gana da Buhari kan babban taron APC na ƙasa.
Jim ƙaɗan bayan haka, shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya gana da shugaba Buhari.
Wata Majiya da muka samu, ta bayyana cewa Buni ya gana da Buhari ne kan babban taron APC na ƙasa, wanda kwamitinsa ke shirin gudanarwa.
Sai dai a wata fira da kafar Talabijin ta ƙasa NTA ta watsa, Shugaban Buhari, yace ya gargaɗi jam'iyyarsa ta APC ta ɗauki lamarin babban taron ƙasa da matukar muhimmanci.
Gwamnatin Ganduje ta haramta Cakuduwar maza da mata a wurin ninkaya, luwadi, Madugo da wasu sabbin dokokin biki
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Ganduje ta hana yara zuwa Otal, Cakuduwar maza da mata a wurin ninkaya, da wasu sabbin dokoki da ya kafa a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wasu sabbin dokoki da suka shafi Otal, wuraren cin abinci da shakatawa da kuma ɗakunan taron biki.
Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta hana shan shisha, zuwan yara Otal, luwadi da madigo da sauran su a baki ɗaya faɗin jihar Kano.
Asali: Legit.ng