Bayan sun sha kashe shi da baki: Buhari zai kammala mulki cike da tarin nasara, Femi Adesina
- Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya magantu a kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sha fama da masu hasashen gobe tun bayan da ya hau mulki
- Sai dai Adesina ya ce duk da hasashensu, ubangidan nasa zai kammala mulkinsa cikin tarin nasara a yan watanni masu zuwa
- Ya kuma bayyana cewar shugaban kasar zai koma mahaifarsa ta daura da kuma mayar da hankali ga dabbobinsa
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu zai kammala wa'adin mulkinsa cikin 'tarin nasara', ya koma mahaifarsa, sannan kuma ya mayar da hankali ga dabbobinsa, cewar mai bashi shawara kan harkokin labarai, Femi Adesina.
Adesina ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'PMB da masu hasashen gobe', wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu.
Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu
Hadimin shugaban kasar ya rubuta:
"Nan da 'yan watanni 17, shugaba Buhari zai sauka lafiya, kamar yadda Allah ya nufa. Zai kammala wa'adinsa cikin tarin nasara, sannan ya koma Daura don kula da dabbobinsa.
"Wannan shine addu'ar miliyoyin mutanen kirki. Kada wani mai kiran kansa da mai karbar wahayi ya yi yunkurin jifarmu da akasin haka. Wa ke maganar karshe? Ubangiji ne ke maganar karshe."
Adesina ya fadi hakan ne yayin da yake bayyana cewa Buhari ya sha fama da masu hasashen gobe tun bayan da ya zama shugaban kasar nan.
Ya kara da cewa:
"Tun bayan da ya zama shugaban kasar, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha fama da masu hasashen gobe. Sun zo da tarin hasashe, wanda da yawa daga cikinsu sun yi nisa da gaskiya."
"Sau da dama, sun kashe shi da baki. Sau da yawa, sun tsige shi harma a zaben 2019. Sun hango rashin lafiya, mutuwa, da fankon kujera a fadar shugaban kasa.
"Amma shekara bayan shekara, wata bayan wata, shugaba Buhari yana ci gaba da ayyukansa na kasa, da kuma iyalansa. Ya dawwama kamar yadda yake Tauraron Arewa.
"Eh, a matsayinsa na dan adam, yana iya yin rashin lafiya lokaci zuwa lokaci. Mun tuna a shekarar 2017, lokacin da Shugaba Buhari bai zauna ba sosai a kasar tsakanin Janairu zuwa Agusta, inda yake dan dawowa kasar a tsakani.
“Mutum, basarake ko talaka, Shugaban kasa ko lebura, na iya yin rashin lafiya, zai iya warkewa, ko ma ya mutu. Abin da ya faru a karshe lamari ne na rahama daga Allah madaukaki”.
Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah
A wani labari, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan ya kammala wa'adin mulkinsa lafiya domin 'tsufa ya fara kama shi', Daily Trust ta ruwaito.
Buhari, wanda ya cika shekaru 79 a ranar 17 ga watan Disamban 2021, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambaya a tattaunawa da aka yi da shi a NTA, a ranar Alhamis.
"Game da shekaru na, ina ganin sa'o'i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta," in ji shi.
Asali: Legit.ng