Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu
- Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar CPC da aka rushe, Saliu Mustapha, ya roki masu takarar kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa da su hakura su mara masa baya
- Abdulaziz Yari, Tanko Almakura, Ali Modu Sheriff na daga cikin manyan 'ya'yan APC da ke hararar kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa
- Sai dai Mustapha ya ce idan har suka mara masa baya ya zama dan takarar jam'iyyar na bai daya, zai yi aiki don ganin nasararta a babban zabe mai zuwa
Abuja - Tsohon mataimakin Shugaban rusasshiyar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) na kasa kuma babban dan takarar kujerar shugaban APC na kasa, Saliu Mustapha, ya nemi sauran yan takara da su janye masa.
Mustapha ya bukaci da su lamunce masa a matsayin dan takara na bai daya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya yi rokon ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, a Abuja lokacin da manyan Jami’an gwamnati daga jihar Nasarawa suka kai masa ziyara.
Sun ziyarce shi ne karkashin jagorancin shugaban APC a karamar hukumar Keffi, Alhaji I. Mohammed Bello Soja, inda suka kaddamar da goyon bayansu kan kudirinsa.
Daga cikin manyan da ke neman kujerar shugbancin jam’iyyar akwai; tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura; tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Sauran sune tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda; tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gorge Akume, Sanata Sani Musa da Sunny Moniedafe.
Mustapha ya ce:
“Ina rokon sauran masu takara da su lamunce mun ko kuma su bani goyon bayansu saboda muna bukatar wasu matakai don bunkasa jam’iyyar. Idan aka bani goyon bayan, zan shirya APC don samun karin nasarori.
“Gwamnatina za ta yi aiki da kowa. Za mu tallata shahararren dan takara kuma Za mu tabbatar da ganin APC ta inganta.”
A halin da ake ciki, The Sun ta rahoto cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Nasarawa, Philip Dada ya nuna goyon bayansa ga takarar Saliu Mustapha a matsayin shugaban APC na kasa.
Ya lamunce mai ne a wani ziyara da ya kai wa tsohon shugaban na jam'iyyar CPC a Abuja.
Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba
A wani labari na daban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja kunne inda ya ce matsawar jam’iyyarsa, APC ba ta gyara duk wasu rigingimun da ke cikin ta ba, jam’iyyar adawa ta PDP za ta amshi mulki a shekarar 2023.
Shugaban kasa Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi wanda NTA ta nuna ranar Alhamis da dare, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban kasan ya kara da cewa ya yi takarar shugaban kasa har sau uku kafin ya samu nasara, don haka duk wani mai son zama shugaban kasa sai ya yi aiki tukuru a kan kudirinsa, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng