Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi
- Manyan jiga-jigan PDP sun nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023
- Cif Raymond Dokpesi, shugaban kwamitin magoya bayan Atiku ne ya zayyana hakan a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu
- Ya ce masu ruwa da tsaki a jihohin kasar 24 sun bayar da cikakken goyon bayansu ga takarar tsohon mataimakin shugaban kasar
Adamawa - Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihohi 24 sun lamuncewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar domin ya dare kujerar shugaban kasa a 2023.
Wani kwamiti da ke goyon bayan takarar dan siyasar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu.
Shugaban kwamitin goyon bayan Atiku, Cif Raymond Dokpesi, ya magantu a yayin da kwamitinsa ya ziyarci garin Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Ya ce Adamawa ce jiha ta 24 da kwamitinsa ke ziyarta kuma cewa dukkanin jihohin sun nuna gagarumin goyon baya ga Atiku, jaridar The Nation ta rahoto.
Dokpesi, wanda ya kafa kamfanin sadarwa ta DAAR, ya yi godiya ga mutanen Adamawa a kan goyon bayan tsohon dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar PDP a zaben 2019.
Ya jaddada cewa rashin tsaro, rashin hadin kai, da rashin aikin yi ne suka sanya kasar ta zama koma baya.
Ya kuma bayyana cewa arewa maso gabas ne kadai yankin da bai samar da shugaban kasa ba tun 1966.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi alkawarin cewa jihar za ta marawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya domin ganin ya cimma kudirinsa na zama shugaban kasa, duba ga cewar shi dan jihar ne.
Fintiri wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, Cif Crowther Seth, ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da marawa Atiku baya don ganin ya dare kujerar.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Tahir Shehu, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Atiku zai ‘yantar da kasar daga rashin ci gaba da rashin tsaro.
Gwamna ya yi watsi da Tinubu Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023
A wani labarin, Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya nuna goyon baya ga tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon SGF, Anyim Pius Anyim, ya zama shugaban ƙasa na gaba daga yankin Igbo.
Punch tace gwamnan ya yi wannan furucin ne a gidansa dake Umuobiakwa, karamar hukumar Obingwa, yayin da ya karbi bakuncin Anyim ranar Lahadi.
Ya bayyana shi da, "Mutum wanda kwarewarsa da gogewarsa ta dace da kujerar shugaban ƙasa a Najeriya."
Asali: Legit.ng