Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa

Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa dake Arewa maso yammacin kasar nan tace nan ba da jimawa ba zata karbi mambobin PDP 4,000
  • Shugaban APC a Jigawa, Sani Gumel, yace masu sauya shekan sun ɗauki matakin dawowa APC ne saboda kyakkyawan jagoranci
  • Ya kuma yi kira ga mambobin APC su fara shirye-shirye yayin da babban taron jam'iyya na ƙasa ke kara kusantowa

Jigawa - Jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Jigawa tace ta kammala duk wasu shirye-shirye na karban mambobin PDP 4,000 zuwa inuwarta.

Shugaban APC na jihar, Alhaji Aminu Sani-Gumel, shine ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai ta kasa, (NAN) ranar Talata.

Yace duk wasu matakai da tsare-tsaren karban masu sauya sheƙan cikin sauki sun kammala, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar
Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sani Gumel ya ƙara da cewa a baya-bayan nan wasu mambobin jam'iyyar PDP sama da 2,000 sun dawo cikin APC a kananan hukumomin Maigatari da Kafin Hausa.

Kara karanta wannan

Ba wani Next Level: PDP ta fusata da yadda APC ke zawarcin Jonathan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace bayan haka ne wasu mutum 4,000 na jam'iyyar PDP suka nuna sha'awar dawowa APC a Garki da kuma Birnin Kudu, kuma ba da jimawa ba za'a shirya taron tarban su.

Gumel yace:

"Shirye-shiryen tarban masu sauya shekan zuwa APC a hukumance ya kusa kammaluwa."

Meyasa zasu sauya sheka zuwa APC?

Sani Gumel yace APC na samun wannan nasarorin ne saboda kyakkyawan jagorancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da kuma gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru.

Yace baki ɗaya mambobin PDP dake shigowa APC na yin haka ne saboda ganin yanayin kyaun gwamnatin APC ta hanyar cika alkawurran da ta ɗauka a ko wane mataki.

Haka nan kuma ya sake jaddada kokarin shugabancin jam'iyya wajen tabbatar da jagoranci na gari da kuma rike wa yan Najeriya amana.

Daga karshe shugaban APC ya yi kira ga mambobin jam'iyya su fara shirye-shirye tun daga mataki na kasa gabanin babban taron APC na ƙasa dake tafe.

Kara karanta wannan

Siyasa: Manyan rigingimun da suka aukawa jam’iyyun PDP da APC a shekarar 2021

A wani labarin na daban kuma Khadijat yar kimanin shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a zaɓen 2023

A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262