Ta kowane hali sai jam'iyyar PDP ta lashe babban zaben 2023, Gwamna

Ta kowane hali sai jam'iyyar PDP ta lashe babban zaben 2023, Gwamna

  • Yayin da zaɓen 2023 ke kara kusantowa, gwamna Wike na jihar Ribas yace PDP ba zata amince da shan kaye ba
  • Gwamnan yace yan Najeriya na shan wahala a wannan yanayin na rashin tsaro kuma PDP ce kaɗai zata iya aikin ceto kasar nan
  • Wike yace kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da gwamnan Abia, Ikpeazu, shi ne yasa ya kai masa ziyarar sabuwar shekara

Abia - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jam'iyyar PDP ba zata taba yarda da shan ƙasa ba a 2023 saboda yan Najeriya sun dogara da ita a matsayin jam'iyyar da zata cece su.

The Nation ta rahoto cewa Wike ya yi wannan furucin ne yayin da ya jagoranci wasu dattawa da jiga-jigan PDP suka kai ziyarar sabuwar shekara ga gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.

Kara karanta wannan

Akwai abubuwa masu kyau dake jiran yan Najeriya a sabuwar shekara, Gwamna Masari

Gwamnan yace yan Najeriya sun zama abin tausayi, waɗan da ba su da wata kyakkyawar makoma a hannun masu garkuwa da yan bindiga.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike
Ta ko wane hali sai jam'iyyar PDP ta lashe babban zaben 2023, Gwamna Wike Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa, waɗan nan yan ta'addan na cigaba da cin karen su babu babbaka ba tare da hukumomin tsaro sun ɗauki mataki a kansu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike ya kara da cewa yan Najeriya na bukatar a kawo karshen halin rashin tsaron da ya addabi kasar nan, kuma PDP kaɗai zata iya aikin.

Yace:

"Wannam ba ita ce ƙasar da muke wa kan mu fata ba, babu wani ɗan Najeriya da zai ce maka yana jin dadin cewa kullum da safe labarin kisa yake fara karya wa da shi."

Meyasa ya kai ziyara jihar Abia?

Gwamnan ya bayyana cewa ya zabi kai ziyara ga takwaransa na jihar Abia ne sabida kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsu a siyasance da kuma abokan taka.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya jingine Atiku, ya bayyana wanda jam'iyya zata baiwa takara daga Arewa a 2023

Ya kuma bayyana gwamna Ikpeazu na jihar Abia a matsayin mutum mai kyawawan halayya, wanda yake taimaka masa idan yana bukata kuma baya barin a ci mutuncinsa.

Kazalika Wike ya bayyana gwamnan da mutum me yaƙini a shirin gyara Najeriya, kuma mai goyon bayan komai domin cigaban ƙasa, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

Jigon jam'iyyar APC, Mista Otu Inyang, ya rasa rayuwarsa bayan wasu yan bindiga sun bude masa wuta a kauyen Ikot Udoma, karamar hukumar Iket, jihar Akwa Ibom.

Rahoto yace Yan bindigan sun bibiyi Jigon APC a jihar suka harbe shi mintuna kaɗan kafin shigar sabuwar shekara yayin da yake kan hanyar koma wa gida bayan halartan addu'o'i a coci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262