Bayan shekaru 6, gwamnatin Katsina ta bayyana lokacin da za ayi zaben kansiloli
- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana lokacin da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar
- Jihar Katsina dai ta ruguje kujerun kansila a jihar tun bayan da ta zargi karkatar da kudin al'umma a bangaren
- A yanzu gwamnati ta ce ta shirya komai tsaf domin gudanar da wannan zabe a kwatan farko na shekara mai zuwa
Jihar Katsina - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a cikin kwatan farko na shekara mai zuwa.
Gwamna Aminu Masari na jihar ne ya bayyana hakan a jiya a wata hira da manema labarai, ya ce an samar da 70% cikin 100% na abin da ake bukata na zaben.
Karo na karshe da aka gudanar da zaben kansiloli shi ne sama da shekaru shida da suka gabata, a lokacin mulkin karshe na jam’iyyar PDP na tsohon Gwamna Ibrahim Shema.
Amma Masari, wanda ya zama gwamna a jam’iyyar APC, ya rusa kujerun kansiloli ne a watan Mayun 2015, saboda zargin karkatar da dukiyar al’umma a matsayin dalilin yin hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masari ya ce an kafa wani kwamiti a karkashin shugaban ma’aikatansa, Muntari Lawal da zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gudanar da zaben.
Ya ce:
“Kashi 70 na abin da ake bukata domin zaben yana nan a kasa, kuma muna fatan gudanar da zaben a cikin kwatan farko na shekara mai zuwa.”
Ya ce an samu jinkirin gudanar da zaben ne saboda shari’ar kotu da PDP ta shigar, kuma gwamnati ba ta so a ci gaba da gudanar da zaben ba saboda shari’ar da ake yi a lokacin.
Jaridar Punch ta ce Masari ya kara da cewa gwamnatinsa ta duba tare da sake tantance ma’aikatan kananan hukumomi sama da mutum 2,000 wadanda a baya gwamnatin da ta shude ta hana su albashi.
Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai
Masari ya kuma ba da shawara kan zaben 2023, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki su sanya Najeriya a gaba akan komai na ayyukansu.
Ya ci gaba da cewa:
“Yayin da muke fuskantar zabukan 2023, ina kira ga shugabanni, galibinsu na addini, na gargajiya, da shugabannin siyasa a kasar nan da su sanya kasar nan a gaba."
Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa
A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga al'ummar jiharsa su mallaki makamai don kare kansu daga hare-haren yan bindiga saboda jami'an tsaro kadai ba zasu iya ba.
Masari, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Muhammadu Buhari House dake Katsina ya ce adadin jami'an tsaron da Najeriya ke da shi ya yi kadan wajen magance wannan matsala.
A cewarsa, ko addini ya amince da mutum ya kare kansa da dukiyarsa daga wanda ke kokarin kwacewa.
Asali: Legit.ng