2023: Masari ya jaddada goyon bayansa kan mika shugabancin kasa kudanci

2023: Masari ya jaddada goyon bayansa kan mika shugabancin kasa kudanci

  • Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya jaddada cewa yana goyon bayan a mika mulkin kasa zuwa kudancin kasar nan
  • Masari ya ce babu inda kundun tsarin mulki ya ce a yi hakan, amma kuma har ila yau bai hana a dinga mulkin karba-karba ba
  • Masari ya ce har yanzu kasar nan matashiya ce, kawai hange da son sauri gare mu, muna son fara gudu tun lokacin rarrafe

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya jaddada matsayarsa kan mika mulkin kasar nan zuwa kudancin kasar nan inda yace hakan zai taimaka wurin karfafa tsarin tarayya ta kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Masari ya sanar da hakan ne yayin martani ga tambayoyin manema labarai yayin taronsu a gidansa ranar Talata.

Kara karanta wannan

Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya

2023: Masari ya jaddada goyon bayansa kan mika shugabancin kasa kudanci
2023: Masari ya jaddada goyon bayansa kan mika shugabancin kasa kudanci. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Bari in sanar da matsaya ta. Wannan kundun tsarin mulkin an yi shi ne domin mu ba mu aka yi wa kundun tsarin mulkin ba. Eh, kundun tsarin mulkin bai ce dole ne mu mika mulki ba, amma me muka karya a kundun tsarin mulkin idan mun mika?
"Har yanzu ina nan kan matsayata a matsayina na Aminu Bello Masari, har sai mun samu siyasa daidaitacciya, ina tunanin mulkin karba-karba a lokuta daban-daban zai taimaka wurin hadin kai. Ina goyon bayan hakan kuma ina nan kan matsayata kuma ina da damar fadin hakan," yace.

Ya yi kira ga 'yan siyasa, manema labarai, shugabannin addinai da na gargajiya da su saka kasar nan farko kafin bukatarsu yayin da zabe ke gabatowa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

"Mu duba siyasa a matsayin hanyar samar da shugabanni karkashin damokaradiyya. Siyasar mu har yanzu matashiya ce, ko bayan samun 'yancin kai zuwa yau, ana batun shekaru sittin kenan, wanda za mu iya cewa lokacin cigaban kasa ne."
"Mu duba inda muke jiya, yau da kuma inda muka nufa gobe, matsalar shi ne muna son mu fara sauri kafin mu gama rarrafe, muna son fara gudu," yace.

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

A wani labari na daban, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce yana sa ran za a ga bayan manyan 'yan ta'addan kasar nan kafin cikar wa'adin mulkin shugaban Buhari.

A yayin jawabi a wani shirin Channels TV, Adesina ya ce da irin kokarin da ake yi na inganta tsaro, za a iya ganin bayan rashin tsaro a cikin watanni 17 da suka rage na mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

"Babu abinda ya gagara," yace.
"A lokuta da dama ina gwadawa da Tamil Tigers na Sri Lanka. Wannan 'yan tawayen sun kwashe shekaru 28, amma wata rana kawai aka ga bayan shugabansu, wanda hakan ya kawo karshensu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng