Jam'iyyar PDP zata lashe jihohi 25 a babban zaben 2023, Sabon Shugaba
- Jam'iyyar PDP ta ƙasa na cigaba da kokarin ɗinke duk wata ɓarakar da ta jawo rikici a baya
- Sabon shugaban PDP na ƙasa, Dakta Ayu, ya tabbatar da cewa jam'iyya ta shirya sake kwace mulkin jihohi 25 a kasar nan
- Yace duk wata ɓara zai tabbatar an dinke ta, kuma shugabancinsa zai tafi da kowa ba tare da nuna banbanci ba
Niger - Sabon shugaban jam'iyyar PDP ta ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya tabbatar da cewa jami'iyyarsa zata sake lashe akalla jihohi 25 na ƙasar nan a 2023.
Dailytrust tace Ayu ya yi wannan furucin ne a wurin taron walima da aka shirya masa a babban filin wasa na Aper-Aku dake Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai.
A jawabinsa yace:
"Mun shirya sake kwace akalla jihohi 25 na ƙasar nan a zaɓen 2023, hakanan kuma mun shiya kwace kujerun majalisun tarayya guda biyu (majalisar dattijai da ta wakilai.)"
"Zamu magance yawaitar ficewar ƴaƴan jam'iyyar PDP zuwa wasu jam'iyyun siyasa. Sannan zamu yi duk me yiwuwa wajen inganta jam'iyya ta yadda mutane zasu rinka sha'awa suna shigowa a dama da su."
Zamu ci nasara a Osun da Ekiti - Ayu
Mista Ayu ya kara da cewa PDP zata bi dare ta yi aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da ta samu nasara a zaɓen gwamna dake tafe a jihohin Osun da Ekiti.
Sai dai ya jaddada bukatar dake akwai na mambobin jam'iyyar PDP su nunka kokarin da suke dan fuskantar kowane ƙalubalen dake tafe.
Kazalika shugaban PDP na ƙasa ya yi dana sanin yadda yan Najeriya da matasan ƙasar nan suka rasa kwarin guiwarsu karkashin mulkin wannan gwamnatin, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Shin Najeriya zata gyaru?
Dakta Ayu ya yi kira ga yan Najeriya kada su cire rai, domin a kwana a tashi wataran Najeriya zata zama ƙasa abin alfahari.
"Najeriya ba zata rabe ba, Najeriya zata cigaba da zama ƙasa ɗaya dunkulalliya, wacce za'a rinka girmamawa kuma ta zamo a gaba-gaba wajen harkokin duniya."
"Zamu tafi da kowane mamban PDP ba wanda za'a ware, wannan ce kaɗai hanyar sake gina jam'iyya. Kuskuren da ya ja mana faɗuwa zaɓe zamu gyara shi."
A wani labarin na daban kuma tsohuwar mai baiwa Buhari shawara kuma shugabar hukumar NIDCOM ta bayyana yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya cece ta lokacin da aka so mata fyaɗe
Shugaban hukumar yan Najeriya dake kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana irin kalubalen da ta shiga ta yadda aka kusa mata fyaɗe lokacin da take aikin jarida.
Tsohuwar yar majalisar tarayya ta shaidawa yan jarida su tashi tsaye kuma su ƙarfafa kansu, su rinka gudanar da binciken kwakkwafi kan wani abu.
Asali: Legit.ng