Rikicin Siyasa: Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya yi murabus daga mukaminsa

Rikicin Siyasa: Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya yi murabus daga mukaminsa

  • Majalisar dokokin jihar Filato ta tsinci kanta cikin rikicin siyasa tun bayan tsige tsohon kakakinta, Honorabul Abok
  • Mataimakin shugaban marasa rinjaye, Philip Dasun, ya sanar da murabus daga kan kujerarsa ranar Talata
  • Yace babu wani rikici a majalisa yanzu, yanzun kowa ya rungumi gaskiya domin abinda ya faru ya isa darasi

Plateu - Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Filato, Philip Dasun, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Dailytrust ta ruwaito cewa ɗan majalisar ya bayyana dalilin aje mukaminsa na majalisa da cewa na kai da kai.

Honorabus Dasun, yana daga cikin makusantan tsohon kakakin majalisa da aka tsige kwanakin baya, Abuk Nuhu Ayuba, kuma ya sanar da murabus ɗinsa ne ranar Talata.

Jihar Filato
Rikicin Siyasa: Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya yi murabus daga mukaminsa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin an kawo karshen rikicin majalisar Filato?

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, Honorabul Dasun yace, "Samun canji na ɗaya daga cikin abubuwan da rayuwa ta ƙunsa."

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Sakataren gwamnati ya yi murabus daga mukaminsa

Dangane da rikicin dake tsakanin ɓangaren su da kuma kakakin majalisa na yanzun, yace:

"Mun fuskanci rikici a majalisa amma yanzun an samu sasanci doka da oda ta dawo."
"Baki ɗayan mu mun dawo kuma mun rungumi gaskiyar cewa mun rasa ɗaya daga cikin mu, babu bukatar cigaba da rikici, wannan kaɗai ya ishe mu darasi."

Hakanan kuma, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Filato, Honorabul Naa’anlong Daniel, a wata hira da manema labarai ya tabbatar da lamarin.

Mista Daniel ya bayyana cewa ya zama wajibi tsohon mataimakin nasa ya yi murabus saboda wasu matakai da jam'iyyar APC ta ɗauka.

Meya jefa majalisar cikin rikici?

Majalisar jihar ta faɗa cikin rikicin siyasa ne tun bayan tsige kakakin majalisa, Honorabu Abok, da kuma maye gurbinsa da Yakubu Sanda.

Kara karanta wannan

Ku kara kaimi wajen fatattakar yan ta'adda a Najeriya, Shugaba Buhari ga Sojoji

Lamarin dai ya kai ga darewar majalisar gida biyu, inda tsohon kakakin ya ja tawagarsa ya cigaba da zaman majalisa, yayin da sabon kakaki ke jagorantar zauren majalisa.

Bugu da kari hukumar yan sanda ta kwace iko da zauren majalisar, tare da bayyana cewa yan majalisan su yi kokarin sasanta kansu.

A wani labarin na daban kuma Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba

Tsohon kwamishina a jihar Cross Riba tare da wasu jiga-jigan APC sun koma jam'iyyar hamayya PDP.

Tsohon gwamna, Donald Duke, da wasu shugabannin PDP a jihar ne suka tarbi masu sauya shekan a sakateriyar PDP dake Kalaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262