Kano da Jihohi 4 da rikicin cikin gida zai iya yi wa Jam’iyyar APC mugun illa a zaben 2023
- Akwai wasu jihohi inda rigimar cikin gida ka iya kawowa jam’iyyar APC cikas a zabe mai zuwa
- Mun kawo jerin wadannan jihohi da ake fama da rikicin cikin gida da; Kano, Kwara, da jihar Osun
- Haka zalika APC na da aiki sosai a gaban ta a jihohin Delta, Ebonyi, Ogun da Ribas kafin zaben 2023
Tun yanzu, an soma yin tankade da rairaya a siyasar Najeriya inda ake ganin rigingimun cikin gida da sauya-shekan ‘yan siyasa daga wata jam’iyya zuwa wata.
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin wasu jihohin da ake hasashen samun matsaloli a dalilin rigingimun da ake samu a cikin gidan APC.
Daya daga cikin jihohin da wannan abin ya yi kamari shi ne Kano, inda a ‘yan kwanakin nan rashin jituwa ta bayyana tsakanin bangaren gwamnati da ‘yan taware.
Jihohin da babu kanta
1. Kwara
A halin yanzu babu zaman lafiya tsakanin bangaren gwamna Abdulrazaq Abdulrahman da na Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed a APC ta Kwara.
Haka zalika babu jituwa tsakanin gwamna mai-ci da manyan ‘ya ‘yan APC irinsu Gbemisola da Saraki wadanda za su iya kawowa tazarcensa barazana a 2023.
2. Gombe
Wani reshen APC da yake cikin matsala shi ne na jihar Gombe, inda a nan ma ake mummunan rikici tsakanin ‘yan gwamna da na Mohammed Danjuma Goje.
Gwamna Inuwa Yahaya da magoya bayansa sun fito karara su na yaki da tsohon gwamnan jihar wanda yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisa.
3. Zamfara
Bayan Inuwa Yahaya, wani gwamna da zai gamu da cikas shi ne Bello Matawalle na jihar Zamfara. Akwai rabuwar kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a Zamfara.
Irinsu Ahmad Yariman-Bakura su na tare da gwamna tun da ya dawo APC, a gefe guda kuma babu jituwa tsakanin tsagin Abdulaziz Yari da na Kabiru Marafa a APC.
4. Osun
A jihar Osun, rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar APC mai mulki. Inda babbar matsalar take shi ne za ayi zaben gwamna a jihar kafin babban zabe na 2023.
Ba a ga maciji tsakanin Gwamna Adegboyega Oyetola da Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola. Sannan akwai ‘yar tsama tsakanin gwamna da irinsu Yusuf Lassun.
5. Kano
A Kano, akwai manyan ‘ya ‘yan APC akalla bakwai da suke adawa da jagorancin Abdullahi Abbas duk da ya na goyon bayan gwamna watau Abdullahi Umar Ganduje.
Masu yakar tsagin gwamnati sun hada da ‘yan majalisu; Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin Sha’aban Sharadan, Tijjani Jobe, da tsohon kwamishina Injiniya Muaz Magaji.
Jihohin da sai an dage
Baya ga wadannan akwai wasu jihohin da ake samun matsaloli a APC irinsu Delta da Ribas da take adawa, sai kuma jihohin da ta ke mulki kamar Ebonyi da Ogun.
Abubuwa sun cabe a jihohi
Ku na da labari rikicin APC sun kara cabe wa bayan an gudanar da zaben shugabanni a watannin da suka gabata. Akalla jihohi 16 ne aka samu sabani bayan zabukan.
APC ta gagara samun hadin-kan ‘ya ‘yanta a kan batun zaben shugabannin mazabu. Akwai jihohin da aka rika harbe-harben bindiga saboda wasu su yi nasara.
Asali: Legit.ng