Yadda jam’iyyar APC ta tsunduma a rikita-rikita a Jihohi 16 bayan zaben Shugabanni

Yadda jam’iyyar APC ta tsunduma a rikita-rikita a Jihohi 16 bayan zaben Shugabanni

  • Rikicin APC sun kara cabe wa bayan an gudanar da zaben shugabanni
  • A makon da ya wuce aka gudanar da zabuka a wasu kananan hukumomi
  • Jaridar This Day ta tattara rahoton irin sabanin da aka gani a jihohi 16

A wasu jihohin, an ki yi zaben, a wasu kuma an buge da rigingimu, a wasu wuraren ‘yan tawaren jam’iyyar sun kawo sabani, sun shirya na su zaben na dabam.

Kamar yadda za a gani, jihohin da ake fama da rigingimu sun hada da Legas, Kwara, Ogun, Sokoto Neja.

Rigimar sakataren rikon kwarya na APC, John Akpanudoedehe da Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio ya fito fili a zaben da APC ta shirya a Akwa Ibom.

A Abia, haka abin ya kasance fada, inda mutanen Donatus Nwankpa da na Ikechi Emenike suka shirya zabuka dabam-dabam, kowa ya fito da shugabanninsa.

Kara karanta wannan

Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Duk da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi yace an yi zaben shugabannin APC lafiya lau, bangaren abokin gabansa, Sanata Magnus Abe ba su shiga zaben ba.

An rasa wa aka zaba a Bayelsa da Enugu

Duk da kotu tace a dakata da zaben APC a Bayelsa, an samu ‘yan taware da suka gudanar da zabe. Timipre Sylva bai samu zuwa ba, amma an ga David Lyon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jihar Enugu kuwa, bangarorin Dr. Ben Nwoye da na Sanata Ken Nnamani sun gudanar da zabuka dabam-daban a daukacin kananan hukumomin jihar.

A Delta ma kotu ta dakatar da zaben shugabannin APC, amma hakan bai hana Sanata Ovie Omo-Agege da mutanensa komai ba, sauran ‘yan APC sun kaurace.

Jam’iyyar APC
Babban gangamin APC Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Meya faru a jihohin Ogun, Osun da Legas?

Har yanzu an gagara shawo kan sabanin Gwamna Dapo Abiodun da Sanata Ibikunle Amosun a Ogun. Hakan ya jawo kowa ya shirya zabensa a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

Kusan haka ya faru a Osun, inda ba a ga maciji tsakanin Rauf Aregbesola da magajinsa, Gboyega Oyetola.

A Legas ma an samu ‘Yan kungiyar Lagos4Lagos da ke karkashin Tunde Balogun sun gudanar da zabuka dabam da sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki.

Adamawa da sauran jihohi

A Imo, magoya bayan gwamna Hope Uzodimma suka shirya zabukan ba tare da shiga bangaren Sanata Rochas Okorocha da na Sanata Ifeanyi Araraume ba.

An samu rahoto gabar Lai Mohammed da AbdulRahman AbdulRazaq ta kara jagwalgwala APC a Kwara. Daily Trust tace an bar magoya-baya suna ta cacar baki.

An samu matsala a jihar Adamawa, tuni irinsu Sanata Aishatu Binani suka soki shirin da APC ta yi. Jaridar tace a wurare da-dama, ba a fara zaben da wuri ba.

Sauran inda aka samu matsala a zabukan sun hada da Sokoto da Neja, inda aka kai ga harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 da Shugaban kasa ya duba kafin ya yi waje da Sabo Nanono da Mamman daga ofis

The Nation tace a Benuwai har magana ta kai kotu inda Dr Wilson Eche, Bartholomew Alike da Eigege Adejo suka nemi ayi watsi da zabukan da aka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel