Siyasar Najeriya: Sakataren gwamnati ya yi murabus daga mukaminsa

Siyasar Najeriya: Sakataren gwamnati ya yi murabus daga mukaminsa

  • Sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi murabus daga kan mukaminsa sabida zai tsaya takara
  • Gwamnan Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya amince da murabus din sakataren, tare da masa fatan alkairi a al'amuransa na gaba
  • Oyebanji, na daga cikin tawagar mutanen da suka yi fafutuka wajen kafa jihar Ekiti shekaru 25 da suka gabata

Ekiti - Sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi murabus daga kan mukaminsa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa, (NAN) tace sakataren watsa labarai na gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Yinka Oyebode, shine ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar.

Oyebode ya kara da cewa gwamna Fayemi ya amince da bukatar sakataren na aje mukaminsa saboda kudirin siyasa.

Gwamna Fayemi
Siyasar Najeriya: Sakataren gwamnati ya yi murabus daga mukaminsa Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yace takardar aje aikin mai ɗauke da kwanan watan 3 ga watan Disamba, zata fara aiki ne daga ranar 7 ga watan Disamba, bayan amincewar gwamna.

Kara karanta wannan

Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

Meyasa ya yi murabus?

A cewar sakataren Fayemi, Mista Oyebanji ya bayyana dalilin murabus dinsa da cewa ya yanke hukuncikin neman takarar gwamna a zaɓen jihar Ekiti dake tafe.

Premium Times ta rahoto Yace:

"Gwamna Fayemi ya amince da murabus ɗin SSG Oyebanji, kuma ya mika godiya ga tsohon sakataren gwamnatin bisa gudummuwar da ya baiwa wannan gwamnatin tun sanda ta ɗare kan mulki a 2018."
"Haka nan kuma gwamna Kayode Fayemi ya yi masa fatan alkairi a dukkan al'amuran da ya saka a gaba."

Mukaman da ya rike a baya

A baya kafin zuwan wannan gwamnatin, Oyebanji, wanda tsohon malamin jami'a ne, ya rike mukamin sakataren gwamnati a lokacin mulkin gwamna Niyi Adebayo.

Kazalika a zamanin mulkin gwamna Fayemi na farko, ya rike ofishin kwamishinan kasafi da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Minista, Sherrif, ya rigamu gidan gaskiya

Oyebanji, shine sakataren tawagar da ta yi fafutukar kafa jihar Ekiti, kuma rahoto ya bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jihar shekaru 25 da suke shuɗe.

A wani labarin na daban kuma Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba

Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, tare da manyan jiga-jigan PDP sun karbi tawagar masu sauya sheka daga APC.

Manyan jiga-jigan APC mai mulki a jihar da suka haɗa da Honorabul Ekbo Okon, Honorabul Wilson Ekpeyong, Honorabul Paul Ogar, Ntufam Asu E. da wasu mutum biyu sun koma tsagin hamayya na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262