Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
- Babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Ondo ta samu gagarumin cigaba a jihar yayin da ake fuskantar babban zaɓen 2023
- Mambobin jam'iyyar ADP karkashin jagorancin shugabansu, Prince Foluso Mayowa Adefemi, sun sauya sheka zuwa PDP
- A cewar mutanen, lokaci ya yi da za'a haɗa karfi da karfe wajen kawo karshen mulkin jam'iyyar APC mara manufa a ƙasar nan
Ondo - Jaridar Leadership ta rahoto cewa kamanin mambobin jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) 10,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo.
Shugaban jam'iyyar, Prince Foluso Mayowa Adefemi, shine ya jagoranci mambobin daga faɗin kananan hukumomi 18 zuwa PDP.
A cewar waɗan da suka sauya shekan, lokaci ya yi da za'a fatattaki jam'iyyar APC daga madafun iko a kowane matakin gwamnati na ƙasar nan.
Hakanan kuma sun ƙara da ikirarin cewa yan Najeriya sun gaji haka nan da mulkin kama karya, wanda babu tsayyayyar manufa mai kyau a cikinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan PDP ya karbi masu sauya shekan
Da yake jawabi a wurin tarban mambobin ADP, jagoran PDP a yankin kudu maso yamma, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya tabbatar wa mutanen suna da rawar takawa a PDP.
Makinde, wanda ya samu wakilcin ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Ondo 2020, Eyitayo Jegede SAN, yace jam'iyyarsu a shirye take ta baiwa mutanen duk wata dama ba tare da nuna banbanci ba.
Bugu da kari ya shaidawa sabbin mambobin cewa babu hayaniya a jam'iyyar PDP, kuma akwai haɗin kai da jawo kowa a jiki.
Ƙun yi abinda ya dace- PDP
Tun da farko, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams, ya yaba wa sabbin yan jam'iyya bisa ɗaukar matakin da ya dace.
Yace:
"Bangaren ilimi, tattalin arziki, ɓangaren lafiya da sauran manyan ɓangarorin ƙasar nan sun lalace karkashin wannan mulkin, kuma duk wani mai tunani dole ya damu sosai."
A wani labarin kuma Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP
Jigon jam'iyyar hamayya PDP a jihar Abia, Dakta Nkole, ya gargaɗi PDP kada ta karbi Sanata Kalu da gwamnan Ebonyi.
A cewarsa waɗan nan mutanen sun gano cewa sun yi kuskuren sauya sheka zuwa APC shiyasa suke son dawo wa PDP.
Asali: Legit.ng