Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau
- Jami’an hukumar filaye na jihar Kano sun kara garkame ofishin lauyan Shekarau, Nureini Jimoh, SAN, jim kadan da samun nasara akan bangaren APC wacce Ganduje ke goyon baya
- An samu rahotanni akan yadda jami’an su ka yi amfani da kwaduna suka rufe ofishin lauyan yayin da shi da sauran abokan aikinsa su ke tsaka da ayyuka a cikin ofishin
- Bayan koken kungiyar lauyoyi ta Najeriya da jama’a, an bude ofishin a ranar sai dai an samu bayanai akan yadda jami’an su ka kara komawa da dare don rufe ofishin
Kano - Jami'an hukumar kula da filaye na jihar Kano sun sake rufe ofishin babban lauya, Nureini Jimoh, SAN, wanda ya wakilci bangaren Shekarau ya kuma yi nasara kan bangaren Ganduje a rikicin shugabancin jam'iyyar APC, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kwana daya bayan samun nasarar a kotu, gwamnatin jihar Kano ta garkame ofishin lauyan da kwado yayin da shi da wasu ma'aikatansa ke ciki suna aiki.
Bayan kungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA, da jama'a a kafafen watsa labarai sun koka kan lamarin, an bude ofishin a ranar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma Daily Nigerian ta bincika ta gano cewa jami'an gwamnatin sun sake dawowa cikin dare sun sake rufe ofishin.
Wata majiya ta ce wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Da safiyar yau, muka samu rahoton yadda gwamnatin jihar Kano ta kara komawa ofishin lauyoyin don garkame ofishin a karo na biyu. Abin ban mamaki shine yadda ofishin ne kadai dokar gwamnatin ta hau kai. Lamarin ya faru ne da dare. Wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano kuma zalinci ne.”
Hukumar kula da filayen jihar Kano a ranar Alhamis ta yi bayani akan wannan aikin inda ta ce ta aikata hakan ne ga mai hayar wurin ba lauyan ba.
Kakakin hukumar, Murtala Umar ya ce:
“Gwamnatin jihar ta garkame wurin wanda Isiyaka Rabi’u & Sons da ke C14/C16 kan titin Murtala Muhammad ne ke hayar wurin.
“Kwamitin ta ba mai wurin gargadi akan wannan wurin tun ranar 14 ga watan Satumban 2021 kuma ta ba shi damar wata daya tana bukatar ya biya kudin hayar wurin tun 2016 zuwa 2021.
“A jiya 1/12/2021, mun garkame wurare talatin daga bangarori daban-daban da ke jihar kamar wasu wurare da ke Zoo road, Zaria road da Ibrahim Taiwo road.”
A cewar kakakin sai da su ka ja kunne kafin su garkame wurin
Ya kara da cewa duk wuraren da su ka garkame a titin Murtala Muhammad sai da su ka ja kunne amma ba su samu wata amsa mai kyau ba. Don haka kwamitin ta yanke shawarar rufe duk wani wuri da bai bi dokokin filaye ba.
Don haka ya ce a matsayinsu na masu kula da filaye, takardu sun nuna musu cewa C14/C16 Isiyaka Rabi’u & Sons ne ke hayar wurin ba Barrista Nuraini Jimo ba.
Asali: Legit.ng