APC za ta ɗaɗaice kafin zaɓen shekarar 2023, Gwamna Wike
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi kiyasi akan lalacewad jam’iyya APC nan kusa ba tare da ta kai labari ba a shekarar 2023
- Gwamnan yace PDP zata fuskanci kalubale iri-iri yayin zaben wanda zai tsaya takarar shugabancin kasa amma hakan ba zai lalata jam’iyyar ba
- Ya bayyana hakan ne yayin wata hirar da gidan talabijin din AIT ta yi da shi a ranar Alhamis, inda Wike ya ce sai mutum ya kai jajirtacce zai iya tsayawa takara 2023 a PDP
Akwai yuwuwar jam’iyyar APC ta tarwatse gaba daya sakamakon kalubalen da za ta fuskanta, ba za ta kai labari ba a 2023, a cewar Gwamna Wike na jihar Ribas, The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya alakanta wannan hangen nasan da ya yi akan cewa jam’iyyarsa ta PDP itama zata fuskanci kalubale iri-iri wurin tsayar da dan takarar shugabancin kasa a 2023, amma hakan ba zai girgizata ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin din AIT a ranar Alhamis inda yace sai tsayayye kuma jajirtacce ne zai tsaya takarar shugaban kasa a PDP a zaben 2023.
Ya ce duk da dai har yanzu jam’iyyar bata yanke shawarar yankin da zata zabo shugaban kasanra ba, amma sai mai jajircewa ne zai iya takara da APC.
Za a ci kwakwa wurin tsayar da dan takarar shugaban kasa
A cewar Wike, akwai aiki mai yawan gaske kafin PDP ta yanke shawarar fitar da shugaban kasa, The Nation ta ruwaito hakan.
Ya kara da cewa:
“Kada wani ya zo yace muku fitar da dan takarar shugaban kasa a PDP karamin aiki ne. Kalubalen da ake fuskanta iri-iri ne. Wanda APC zata fuskanta rusata zai yi yayin da PDP kuma zata iya shanyewa.
“PDP ta kara dawo wa da kanta martaba a idon ‘yan Najeriya. Don haka yadda kimar APC ta zube kowa zai so ya koma PDP.”
Wike ya ce sai ya duba kafin ya ba wani goyon baya wurin tsayawa takara
Wike ya ce zai bayar da goyon baya ga shugaban kasan da zai tallafa wa kowa ba wai ya mayar da hankalinsa akan kansa ba
Don haka inji Wike, idan mutum ya na so ya goyi bayansa a PDP, sai ya kasance jajirtacce don ya fuskanci azzalumar jam’iyya irin ta APC.
Wike ya ce ya ji dadin yadda PDP ta sauya salo ta hanyar samar da kwamitin ayyuka na kasa, NWC.
Asali: Legit.ng