An gano ranar da APC ta ke hari domin shirya zaben sababbin Shugabannin Jam’iyya na kasa
- Shugabannin APC su na daf da sa lokacin da za ayi zaben sababbin shugabannin jam’iyya na kasa
- Wata majiya tace za a gudanar da babban gangamin jam’iyya ne a farkon Fubrairun shekarar 2022
- Tun 2020 da aka ruguza majalisar Oshiomhole, aka bar jam’iyyar a hannun kwamitin rikon kwarya
Abuja - Legit.ng ta samu kishin-kishin cewa an tsaida magana a game da lokacin da jam’iyyar APC za ta gudanar da babban gangaminta na kasa a shekarar 2022.
Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021, ta na cewa an zabi ranar da ake sa ran za a shirya zaben sababbin shugabannin jam’iyyar APC.
Wani daga cikin manya a sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a birnin tarayya Abuja, ya shaidawa jaridar cewa ana tunanin za ayi zaben ne a watan Fubrairu.
Idan hakan ta tabbata, za a gudanar da babban gangamin ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Fubrairu, 2021.
Da yake magana da manema labaran, wannan jigo na jam’iyya da ba a kama sunansa ba, yace a halin yanzu ana tunanin ayi zaben a farkon Fubrairun shekarar badi.
“Yanzu mu na tunanin za a yi amfani da ranar 6 ga watan Fubrairu domin ayi zaben.” – Majiya.
Zama da shugaban kasa
A ‘yan kwanakin nan ne kwamitin rikon kwarya da shirya babban zabe na APC da ke karkashin gwamna Mai Mala Buni suka gana da shugaban kasa a kan batun.
Sai dai ba a iya tsaida wata rana a lokacin da aka yi zama da Mai girma Muhammadu Buhari ba. Ana sa ran bada jimawa ba, za a bada sanarwar ranar da aka zaba.
Babu majalisar NWC tun 2020
Idan an yi nasarar shirya wannan zabe kamar yadda ake sa rai, APC za ta samu majalisar NWC na farko tun bayan fatattakar Adams Oshiomhole a watan Yunin 2020.
Adams Oshiomhole ya karbi rikon jam’iyyar ne a 2018 bayan an yi waje da John Oyegun. Daga kafuwarta a 2013 zuwa yanzu, APC dai ta yi shugabanni akalla hudu.
Bola Tinubu da zaben 2023
A baya an ji cewa kungiyar masoya ta Edo Volunteers for Tinubu 2023 sun yi alkawarin idan sun samu dama, za su sayawa Bola Tinubu fam, ya nemi shugaban kasa.
Haka zalika wani dattijo mai shekara kusan 100 a Duniya, Pa Raphael Okeowo yace Ubangiji ya yi masa nuni, ya ga tsohon gwamna Tinubu a kan kujerar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng